Gasar Kayan Dandano Na Onga ‘Taste The Milions’ Yana Canza Abinci Zuwa Nau’ika Da Yawa

Bikin garabasar kayan dandano na Onga mai taken ‘Taste the Milions Promo’ na ci gaba da samar da farin ciki, ga dubban masu amfani da shi cikin aminci da suka koma dafa abinci domin samun nasara mai canza rayuwa.

Gasar Kayan Dandano Na Onga ‘Taste The Milions’ Yana Canza Abinci Zuwa Nau’ika Da Yawa

Bikin garabasar kayan dandano na Onga mai taken ‘Taste the Milions Promo’ na ci gaba da samar da farin ciki, ga dubban masu amfani da shi cikin aminci da suka koma dafa abinci domin samun nasara mai canza rayuwa.

Onga ya samar da mutane da suka samu nasara sama da 4,027 a cikin ‘yan makonni kadan, daga iyalai waxanda a dalilin haka ne yin murmushi ga kananan ‘yan kasuwa wadanda suka cimma muradunsu ta hanya gaskata mafarkinsu. Wannan ita ce damar ku don shiga jerin masu ci gaba da samun girma!

A yayin da aka zauna domin tantancewa a baya-bayan nan, wata daga cikin wacce ta yi mai suna Faith Susan daga Jihar Ogun, wadda ta samu kyautar zunzurutun kuxi Naira miliyan xaya, ta bayyana farin cikinta:

“Sau uku ina shiga wannan gasa, kuma ba taba zaton zan yi nasara ba. ian godiya ga Onga sosai! ”… Juriyarta ta biya, kuma yana iya zama labarinku na gaba!

A karkashin kulawar da ta dace na wakilai daga Hukumar Kula da Lottery ta Kasa, Hukumar Kare Gasar Tarayya da Kare masu amfani da Kayayyaki, da Hukumar Kula da tsatace Kaya ta Jihar Legas, Onga ya sanar da waxanda suka yi nasara a mako 8, tare da kare mutuncin mai talla.

Daga cikin wadanda suka yi nasarar samun babbar kyautar Naira miliyan 1 akwai Edwin Gabriel da Helen Edem Sunday daga Akwa-Ibom, Fatima Adam daga Jos, da Anyanwu Pearl daga Kaduna. Wadannan kadan ne daga cikin ‘yan Najeriya da yawa wadanda rayuwarsu ta canza, kuma kuna iya zama kamar su nan gaba.

Bayan manyan kyaututtukan, Onga yana ba wa daruruwan masu amfani da kaya kyauta a kowane mako tare da kyaututtuka masu ban mamaki: wadanda suka yi nasara su 82 sun dauki na’urori na gida don habaka gasar dafa abinci, kuma akwai wadanda suka yi nasara 50 yanzu suna jin dadin sabbin injin dafa abinci don dafa abinci.

Mutane 160 da suka yi nasara sun sami Naira 10,000 kowannensu don faranta musu, kuma an bai wa mutum 20 wadanda suka yi nasara kyautar Naira 50,000 kowanne.

Sannan mutum 5 da suka yi nasara sun samu kyautar Naira 500,000 kowanne, kuma babbar kyauta, Naira miliyan 1, na ci gaba da haifar da lokutan da ba za a manta da su ba!

Lillian Omorenuwa, Manajan Kula da sashen ‘Culinary, Promasidor Nigeria, ya yaba wa ‘yan Najeriya bisa ci gaba da goyon bayan da suke bayarwa.

Ta ce “Muna son shiga da yawa da kuma labaran farin ciki wadanda suka ci nasarar a gasarmu suna rabawa. Daga jadawalin farko zuwa yanzu, mun samu wadanda suka yi kudi 65, 33 daga cikinsu sun ci Naira 500,000, sai kuma 65 sun ci Naira 100,000, yayin da 260 suka samu kayuatar Naira 50,000, akwai kuma 2115 sukuma sun samu Naira 10,000, da kuma adadin mutum 1,491 da suka ci blender da gas cookers.

Har yanzu muna da kyaututtuka masu ban mamaki da ke jiran a wadanda suka yi nasara, kuma muna sa ran mayar da ’yan Najeriya da yawa a matsayin miloniyoyi yayin da ake ci gaba da tallatawa.”

Ademola Ologbe, Mataimakin Manajan Samfurin Abinci, na Promasidor Nigeria, ya kara da cewa zanen raffle ya kasance mai sauki kuma zai ci gaba da rike wannan matsayi.

Ya kuma kara da cewa “Idan kuka kara shiga, za a kara samun damar yin nasara kamar daya daga cikin wadanda suka ci Naira miliyan daya.”

Kasancewa yana da sauƙi kamar siyan fakitin naman sa Onga ko Chicken 90 cubes, ko fakiti biyu na Onga naman sa ko kaji 50 cubes, musayar fakitin fanko don katin kati, zazzagewa don bayyana lambar musamman, da aika shi zuwa 1393. Tare da wannan tsari mai sauƙi, kowa zai iya zama mai nasara na gaba.

Tare da jimillar kyaututtukan da suka kai Naira miliyan 250, da suka hada da girki, injina, katin waya, da tukuicin kudi, ‘Taste the Millions promo’, biki ne na nuna aminci da amanar da iyalai na Nijeriya suke da shi ga Onga.

Yayin da tallan ya kusa kai wa karshe, Onga ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan damar su shiga sahun masu nasara.

Don karin bayani da sabuntawa kan masu cin nasara, masu amfani da kayanmu za su iya bin Onga akan kafofin sada zumunta (IG:@onga_nigeria, FB: @Onga Nigeria, X: Onga Nigeria, TikTok: Onga.Nigeria) ko a ziyarci www.ongamillionspromo.com

Dangane da tarihin ‘Promasidor Nigeria Limited’ kuwa

Robert Rose ne ya kafa Promasidor a 1979 wanda ya bar Burtaniya a shekarar 1957 zuwa Zimbabwe don cim ma burinsa na Afirka.

Ya girma tare da kasancewarsa a cikin kasashe sama da 30 na Afirka.

Promasidor Nigeria ta samu gagarumin ci gaba tun lokacin da ta fara aiki a shekarar 1993 tare da ‘tambarin tutar’ Cowbell ya zama sunan gida a gidajen Najeriya.

Promasidor yana samarwa, rarrabawa, da kuma tallata nau’ikan samfura masu inganci kamar kayan dandanon na Onga, samfuran kiwo na Cowbell da Abubuwan sha, samfuran Loya & Miksi Kiwo, Top Tea, Twisco Cocoa Beverage, da Kremela a duk fadin kasar, sun kawo farin ciki ga miliyoyin masu amfani da su. Madararsa ta gari, kayan abinci da abin sha suna da araha, masu dadi, kuma masu kyau ga kowa.