Gasar Kofin Duniya: Ingila ta tumurmusa Iran a wasan farko

Iran ta zare kwallaye biyu daga cikin shidan da Ingila ta jefa mata.

Gasar Kofin Duniya: Ingila ta tumurmusa Iran a wasan farko

‘Yan wasan Ingila suna murna

Ingila ta fara gasar Kofin Duniya da kafar dama bayan da ta tumurmusa tawagar Iran da ci 6-2 a fafatawar da suka yi a birnin Doha.

Jude Bellingham ne ya fara ci wa Ingila kwallonta ta farko kafin daga bisani Bukayo Saka da Raheem Sterling suka ci ta biyu da ta uku kafin a je hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne Bukayo Saka ya kara ta hudu kuma ta biyu a wajensa, Iran ta bai wa magoya bayanta kwarin gwiwa a minti na 65 bayan da Mehdi Taremi ya ci musu kwallo daya.

To sai dai murnar ta koma ciki bayan da Marcus Rashford ya kara wa Ingila kwallo ta biyar a karawar, daga nan kuma Jack Grealish wanda ya shigo daga baya ya kara ta shida.

An daf da tashi daga karawar ne Iran ta samu bugun fenareti inda ta samu nasarar zura kwallo ta biyu a fafatawar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos