Gasar Kofin Duniya: Sarkin Qatar ya koka da sukar da kasar ke sha

Qatar ta narka biliyoyin daloli a shirye-shiryen daukar nauyin Gasar Cin Kofin Duniya.

Gasar Kofin Duniya: Sarkin Qatar ya koka da sukar da kasar ke sha

Agogon lissafin loacin Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 a Doha, babban birnin kasar Qatar. (Hoto: KARIM JAAFAR/AFP)

Sarkin Qatar Sheikh Tamin bin Hamad Al Thani ya koka da irin suka da kasar ke sha daga ‘yan gaza gani kan batun gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a kasar.

A cewar Al Jazeera, tun lokacin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta ayyana kasar a matsayin wacce za ta karbi bakuncin gasar a 2010, Qatar take narka biliyoyin daloli a shirye-shiryen daukar nauyin gasar.

Tun daga lokacin kuma kasar take ta fuskantar suka da tuhume-tuhume daban-daban, kama daga bakin ma’aikata da za ta dauka, zuwa kare hakkin mata har masu goyon bayan ‘yan luwadi da madigo.

“Tun da muka yi nasarar samun wannan damar ta daukar nauyin wannan gasar, aka yi wa Qatar rubdugu da sukar da babu kasar da aka taba yi wa haka,”  in ji sarkin a jawabinsa ga Majalisar Kasar.

Shi kuwa Shugaban FIFA, Gianni Infantino cewa yake, wannan gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Gabas ta Tsakiya, za ta kasance wadda ta fi duk wadanda aka taba yi a shekarun baya.

Za a soma gasar Cin Kofin Duniya ce a ranar 20 ga watan Nuwambar 2022.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno