Gasar kwallon Tenis ta Afirka: dan wasa kuadiri ne zai jagoranci tawagar Najeriya a Tunusiya
dan wasan kwallon Tenis din nan da ya lashe gasar gwajin kwallon tenis da aka gudanar a otel din Country Club da ke unguwar Ikeja a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata, mai suna Oyinlomo Aruna kuadri shi zai jagoranci tawagar ’yan kwallon tenis da za su wakilci Najeriya a gasar kwallon tenis […]
dan wasan kwallon Tenis din nan da ya lashe gasar gwajin kwallon tenis da aka gudanar a otel din Country Club da ke unguwar Ikeja a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata, mai suna Oyinlomo Aruna kuadri shi zai jagoranci tawagar ’yan kwallon tenis da za su wakilci Najeriya a gasar kwallon tenis ta kasashen Afirka da za a gudanar a Tunisiya a watan da muke ciki.
Tawagar da ta kunshi ’yan wasa takwas da za su wakilci Najeriya a gasar tuni suka tashi daga filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja inda suka bi ta kasar Moroko suka zarce kasar Tunusiya inda za a gudanar da gasar.
Tawagar ta kunshi shugaban tawagar kuadri da Angel McCleod da Blessing Patrick da Tmipre Godsgift da Micheal Oshewa da Micheal Ayoola da kuma Martins Abamu. Mai horar da ’yan kwallon tenis rukunin matasa, Muhammed Ubale ya bayyana cewa kwararriyar ’yar kwallon tenis Adetayo Adetunji za ta bi sahun takwarorinta daga kasar Afirka Ta Kudu inda take zaune.
A wasan gwajin da aka gudanar na ’yan kasa da shekaru 14 da 16 dan wasa Christopher Bulus ya lallasa Abamu da ci 4-1 da 2-4 da kuma 5-10.
Amma dan wasa Oshewa da dan wasa Ayoola sun samu nasarar kaiwa ga mataki na kusa da karshe.