Gasar La-Liga: Gobe za a kece-raini tsakanin Real Madrid da Balencia
A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga, a gobe Asabar da misalin karfe 8:45 na dare za a kece-raini a tsakanin kulob din Real Madrid da Balencia. A kakar wasa ta bana, kulob din Real Madrid dai yana cikin matsala don ko a makon jiya sai da […]
A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga, a gobe Asabar da misalin karfe 8:45 na dare za a kece-raini a tsakanin kulob din Real Madrid da Balencia.
A kakar wasa ta bana, kulob din Real Madrid dai yana cikin matsala don ko a makon jiya sai da kulob din Eibar ya doke shi da ci 3-0. Kulob din Balencia ma yana cikin matsala saboda kawo yanzu shi ne na 11 a teburin gasar bayan ya hada maki 17 a wasanni 13.
A wasan na gobe za a hadu ne da Madrid da ke matsayi na 6 da maki 20 da Balencia da ke matsayi na 11 bayan ta hada maki 17.
Ana sa ran masoya kwallon kafa za su yi tuturuwa a gidajen kallon kwallo don ganin yadda wannan wasa zai kaya.
A jibi Lahadi kuma kulob din FC Barcelona zai hadu da na Billareal duk a gasar ta La-Liga.
Idan za a tuna, a ranar Asabar da ta wuce kulob din Atletico Madrid ya yi kunnen doki da na FC Barcelona da ci 1-1.
Kawo yanzu kulob din Sebilla ne yake saman teburin gasar da maki 26 sai FC Barcelona na biyu da maki 25 sai Atletico Madrid a matsayi na uku da maki 24 sai kulob din Alabes da ke matsayi na 4 da maki 23.