Gasar MTN/Kannywood Award 2014 ta zama Baya ba Zane!

Cikin dare sosai wani dan jarida ke fada min sakamakon gasar MTN/Kannywood Award 2014,amma sai da na kasa hakuri saboda ban ga carki haye manya ba, watau Adam A Zango ba a cikin wadanda suka samu nasarar lashe gasar. Na ce ya turo min sakamakon a dandalin sada zumunta na facebook.Da dai ban so yin […]

Gasar MTN/Kannywood Award 2014 ta zama Baya ba Zane!
Gasar MTN/Kannywood Award 2014 ta zama Baya ba Zane!

Cikin dare sosai wani dan jarida ke fada min sakamakon gasar MTN/Kannywood Award 2014,amma sai da na kasa hakuri saboda ban ga carki haye manya ba, watau Adam A Zango ba a cikin wadanda suka samu nasarar lashe gasar. Na ce ya turo min sakamakon a dandalin sada zumunta na facebook.Da dai ban so yin magana kanta ba, saboda ta wuce, amma irin yadda na tsaya na auna ta waccan shekarar da wannan, da kuma yadda mahassadan Zango ke ta dariyar wai tauraruwarsa ta rage haske, shi ya

sa na ce to bari in yi wa tufkar hanci.
A ganina gara gasar waccan shekarar da wannan, domin kuwa zalunci da son rai da rashin gaskiya sun bayyana karara a cikinta, duk da waccan ma an taba magudi, kamar yadda aka saba a Nijeriya. Duk mai hankalin da ya ga tsarin yadda ake yin ta ya san akwai lauje cikin nadi. Idan ba haka ba, wanda hakan ne ma ya sa aka ware wasu jarumai daban aka ba su kyautar rukunin zaben ’yan kallo (choice award), amma kuma ba a bayyana makin da kowa ya samu ba, da kuma wanda ya doke, tunda har MTN din ya rika cazar mutane kudi; tsarin kuma da ba a yi irinsa a bara ba? Kuma ina irin kyautar da aka ba Sani Danja a baran ta jarumi mafi kayatarwa? Ko don dai ana tunanin Adamun ne kadai ya dace da ita, shi ya sa ta yi layar zana?
Hakazalika an kara yin biris da tsarin karrama tsofaffin da suka dade suna ba da gudunmuwarsu a harkar fim, wadda ita ma aka yi a bara, inda aka karrama irin su Samanja da Abdu Kano karkuzu da kasimu Yero da dai sauransu; ko ana nufin sun kare ne, ko kuwa wani wasan kwaikwayo ne aka yi da hankullan jama’a? Wannan kadai manuniya ce da ke gwada wa duniya cewa masu shirya gasar irin sammakon balbelu suka yi, watau na banza, don sun dade suna shirin yin gasar, amma kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu.
Haukan da wsu ke yi na ganin Adaam A. Zango bai kamata ya ci gasar ba ya bayyana ne a daidai lokacin da fim din da ya shiga gasar na ‘Saki Kowa’ aka bi kyaututtuka har guda uku da shi a bangarorin waka da siddabaru da kuma hada hoto, kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito.Idan kuwa maganar kayatarwa ake yi, to ba shakka a fin din ‘Basaja Takun karshe na Adamu ya kai matuka wajen farin jini da kayatar da ’yan kallo, wanda kowa ya tabbatar a duk dan tsakanin nan ba a yi wani fim ba da ya kai shi daukaka ta kowane bangare ba. Bisa wannan dalilin ma ne yaron Adamun Mustapha Naburaska ya zama gwarzon matallafin jarumi, to kuwa waye kayataccen jarumin idan ba Adam A. Zango ba?
Kada a manta Zango ko a waccan shekarar shi ne ya zama gwarzon makadi da fim din Basaja, kuma ko a wajen wannan gasar ma yana cikin masu nishadantarwa, amma aka yi masa haka.
Abin da ya kamata kowa ya sani, shi ne, Adamu yanzu ya zama alkamar bisa dutse,wadda Allah ke ba ta ruwa, don kuwa da kayuta ko babu shi ake so, ake ya yi, kuma shi kadai ne tauraruwarsa ke haskaka masana’antar, idan an yi gardama a kalli tallar fim din “Gwaska” kai za a iya bambacewa tsakanin aya da tsakuwa. Kuma shi ba bakon kyauta ba ne, domin shi ta Kwankwasiyya ma ya lashe. Don haka duk kiyayyya da hassadar da ake nuna masa ba komai take kara masa ba sai daukaka da fari fat din farin jini.

Kwamared Kabir Sa’idu Dandagoro (Bahaushe) 08038387516 -kibdau:[email protected].

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu