Gasar Taslim Thunder Balogun ta shiga zagaye na 16
Gasar kwallon kafa ta cin kafin kalubale na ’yan kasa da shekaru 17 da ake gudanarwa a jihar Legas ta shiga zagaye na 16 bayan da kungiyoyi daban-daban suka fafata da juna. Gasar wacce aka yi mata lakabin, Gasar cin kalubale ta ’yan kasa da shekaru 17 ta Taslim Thunder Balogun ana gudanar da ita […]
Gasar kwallon kafa ta cin kafin kalubale na ’yan kasa da shekaru 17 da ake gudanarwa a jihar Legas ta shiga zagaye na 16 bayan da kungiyoyi daban-daban suka fafata da juna.
Gasar wacce aka yi mata lakabin, Gasar cin kalubale ta ’yan kasa da shekaru 17 ta Taslim Thunder Balogun ana gudanar da ita ne a filin wasa na Taslim Balogun da ke jihar Legas.
Babu shakka gasar ta kayatar da ’yan kallo inda wasu da dama daga cikin kungiyoyin da suka fafata suka nuna bajinta.
Sai dai kungoyin da suka haye zagaye na 16 sun hada da kungiyar kwallon kafa ta bictory FC da kungiyar Nero FC da kuma kulab din Teslim Balogun FC. Sauran kungiyoyin kwallon kafar su ne Mighty Blaster da kulob din United FC da kuma na Flying Hawks.
daya daga cikin mutanen da suka shirya gasar, mai suna Omotayo Ashiru ya shaida wa manema labarai cewa sauran kungiyoyin da za su fafata a zagaye na 16 sun hada da wadanda suka yi nasu wasan a cibiyoyin jihar daban-daban.
‘Mun kammala dukkanin wasannin cibiyar Ikorodu inda kungiyoyi guda takwas suka samu nasarar tsallake wa zuwa zagaye na gaba. Muna sauraron sauran cibiyoyin kafin mu ci gaba da zagaye na 16’. Inji shi.
Omotayo ya bayyana cewa wadanda suka shirya gasar sun gano yara masu kwazo da za su mika sunayensu ga hukumar kwallon kafa ta jihar Legas don sanya su a wadansu shirye-shiryen na gaba.
Tuni dai kungiyoyi da ke cibiyar birnin Ikko suka fafata da juna inda kungiyar kwallon kafa ta Songs FA ta kara da Samadeck FC sai kulob din Dreams Teams FC ya kara da na 36 Lion FC.