Gasar UEFA Champions League: Gobe za a yi wasan karshe tsakanin Jubentus da FC Barcelona
A gobe Asabar 6 ga watan da muke ciki ne za a yi wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da (UEFA Champions League) a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Jubentus da ke Italiya da kuma ta FC Barcelona da ke Sifen. Wasan zai yi armashi ganin dukkan […]

A gobe Asabar 6 ga watan da muke ciki ne za a yi wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da (UEFA Champions League) a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Jubentus da ke Italiya da kuma ta FC Barcelona da ke Sifen. Wasan zai yi armashi ganin dukkan kungiyoyin biyu suna tashe a kakar wasa ta bana, bayan sun lashe manyan kofuna bibbiyu a kasashensu.
Yayin da Jubentus ta lashe kofunan gasar rukuni-rukuni na kasar da aka fi sani da Serie A da kuma ofin kalubale (Italian Cup) a halin yanzu, ita ma FC Barcelona tuni ta lashe manyan kofuna biyu watau na La-Liga da ke Sifen da kuma na Copa Del Rey. Kenan dukkan kungiyoyin biyu sun lashe kofuna bibbiyu kuma suna hankoron lashe na uku a wasan gobe.
Wasan zai gudana ne a Berlin da ke Jamus a filin wasan da ake kira Olympiastadion da misalin karfe takwas saura kwata agogon Najeriya.
Miliyoyin masu sha’awar kallon wasan kwallon kafa a sassan duniya ciki har da Najeriya ne ake sa ran za su kalli wasan a akwatunan tabalijin. Tuni gidajen da ke nuna kallon kwallo a Najeriya suka fara shirye-shiryen karbar dubban ’yan kallo. Ana sa ran gidajen kallon za su cika makil musamman ganin yadda kowane bangare ke da dubban magoya baya.
Tuni masu sha’awar kallon kwallo a Najeriya suke ta sharhin yadda wasan zai gudana. Yayin da wadansu ke ganin Jubentus ce za ta samu nasara a wasan, musamman ganin wannan shi ne karon farko tun cikin 1996 da kulob din ya dauki kofin, wadansu kuma sun ce kulob din FC Barcelona ne zai samu nasara a wasan, musamman ganin yadda kulob din yake tashe a kakar wasa ta bana. Sannan FC Barcelona ce ta lashe kofin a shekarar 2011 watau kimanin shekaru hudu da suka wuce.
Kulob din Jubentus yana tinkaho da zaratan ’yan kwallo irin su Tebez da Morata da Chellini da Pogba da sauransu, yayin da FC Barcelona kuma yake tinkaho da Messi da Neymar da Suarez da Iniesta da sauransu.