Gasar Wasanni ta Afirka: Najeriya ta doke Ghana da ci 2 -0
Matasan ’yan kasa da shekara 23 da ke wakiltar Najeriya a wasan kwallon kafa sun doke takwarorinsu na Ghana da ci 2-0 a gasar wasannin Afirka da ake yi a Congo Brazzabille.Najeriya ta zura kwallonta ta farko ne a ragar Ghana ta hannun Junior Ajayi a minti na 10 da dawowa daga hutun rabin lokaci, […]
Matasan ’yan kasa da shekara 23 da ke wakiltar Najeriya a wasan kwallon kafa sun doke takwarorinsu na Ghana da ci 2-0 a gasar wasannin Afirka da ake yi a Congo Brazzabille.
Najeriya ta zura kwallonta ta farko ne a ragar Ghana ta hannun Junior Ajayi a minti na 10 da dawowa daga hutun rabin lokaci, sannan Kingsley Sokari ya kara ta biyu saura minti uku a tashi daga wasan.
A wasan farko Najeriya ba ta kara da Masar ba, saboda janyewar da Masar ta yi daga gasar daf da za a fara wasannin. Ita kuma Ghana ta tashi wasa canjaras ba ci ne da kasar Senegal a ranar Lahadi.
A gobe Asabar Najeriya za ta buga wasan gaba da kasar Senegal, yayin da Ghana ta kammala wasannin rukuni na biyu da maki daya kacal, kamar yadda gidan rediyon BBC Landan ya ruwaito.
Daf da karshen watan Agustan bana, Masar ta ce ta janye tawagar kwallon kafa ta mata da ta maza daga shiga wasannin na Afirka ba tare da ta bayar da wani dalili ba.