Gasar zakarun kulob-kulob na Turai: Arsenal ta nuna da gaske take
Ga dukkan alamu kakar wasa ta bana za ta yi wa kulob din Arsenal da ke Ingila kyau ganin yadda kulob din yake haskakawa a gasar zakarun kulob-kulob a Nahiyar Tura (Champions League).Ya zuwa ranar Talatar da ta wuce kulob din ya lashe wasanni biyu da ya buga a gasar da hakan ta sa yake […]

Ga dukkan alamu kakar wasa ta bana za ta yi wa kulob din Arsenal da ke Ingila kyau ganin yadda kulob din yake haskakawa a gasar zakarun kulob-kulob a Nahiyar Tura (Champions League).
Ya zuwa ranar Talatar da ta wuce kulob din ya lashe wasanni biyu da ya buga a gasar da hakan ta sa yake saman tebur a jerin kungiyoyin da suke fafatawa a gasar a rukunin F.
Yanzu haka kulob din ya hada maki shida daga wasanni biyu da ya yi.
Shahararren dan kwallon Real Madrid a da, Mesut Ozil wanda ya canza sheka a ranar da aka rufe kakar saye da sayar da ’yan kwallo yana daga cikin ‘yan kwallon da suke taimakawa kulob din wajen samun nasara a wannan lokaci.
Hasalima, masana harkar kwallo sun tabbatar dan kwallon ne ya ba takwarorinsa ’yan wasan kulob din Arsenal kwarin gwiwar lashe wasanni a kan kari tun bayan da ya fara yi wa kulob din wasa a kakar wasa ta bana.
Masana harkar kwallo sun ce ba karamin kuskure kulob din Madrid da ke Sifen ya yi ba na sayar da Mesut Ozil ga Arsenal a kakar wasa ta bana ba, ganin yadda dan kwallo ne da ke da hazaka da kuma iya taka leda a duk lokacin da yake wasa.
Masana sun yi hasashen muddin kulob din na Arsenal ya cigaba da nuna kwazo kamar yadda yake yi a halin yanzu a gasar, babu shakka zai iya lashe kofin a karon farko tun bayan da kulob din ya taba kai wa ga wasan karshe a shekaru da dama da suka gabata.
Haka abin yake a gasar rukuni-rukuni na Ingila, inda kulob din Arsenal a yanzu haka yake saman tebur da yawan maki 15.
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa na kulob din sun yi hasashen muddin kulob din ya cigaba da nuna kwazo a gasar, babu shakka zai iya lashe kofin Premier a wannan karo.
Kimanin shekara takwas kenan rabon da kulob din Arsenal ya lashe kofi sai dai akwai yiwuwar ta sake zane a wannan karon ganin yadda kulob din yake haskakawa a wasannin da yake fafatawa.