Gasar Zakarun Turai: Wasannin da za a fafata a ranar Talata
Za a ci gaba da wasa na hudu-hudu a cikin rukuni a gasar Zakarun Turai wato Champions League ranar Talata, inda za a yi karawa takwas. Za a buga wasannin ne da misalin karfe karfe 8:00 na dare. Sai dai tuni aka yi nisa a wasan Manchester City da FC Copenhagen wanda aka fara tun […]
Za a ci gaba da wasa na hudu-hudu a cikin rukuni a gasar Zakarun Turai wato Champions League ranar Talata, inda za a yi karawa takwas.
Za a buga wasannin ne da misalin karfe karfe 8:00 na dare. Sai dai tuni aka yi nisa a wasan Manchester City da FC Copenhagen wanda aka fara tun da misalin karfe 5:45 na Yammacin Talatar nan.
- Kwadayin kudi ke kai wasu ’yan kwallon Firimiyar Ingila —Kroos
- Ranar Yara Mata: A Najeriya aka koyar da mu kamar ’ya’yan turawa —A’isha Isma’il
Ga rukunai da kungiyoyin da za su fafata a daren:
Rukuni na 5
Ac Milan vs Chelsea
Dinamo Zagreb vs Red Bull Salzburg
Rukuni na 6
Celtic da RB Leipzig
Shakhtar Donetsk da Real Madrid
Rukuni na 7
FC Copenhagen da Manchester City
Borussia Dortmund da Sevilla
Rukuni na 8
Paris Saint-Germain da Benfica
Maccabi Haifa da Juventus
Ana dai ganin cewa, wasan da zai fi zafi a rukuni na biyar shi ne fafatawar da za a yi tsakanin AC Milan da Chelsea.
A rukuni na shida kuwa, wasan da zai fi daukar hankali shi ne wanda za a gwabza tsakanin Real Madrid mai rike da kofin da Shahktar Donetsk da.
Wasan da za a kai ruwa rana tsakanin Sevilla da Borussia Dortmund shi ne zai fi daukar hankali a rukuni na bakwai.