Gaskiya da rikon amana ne sirrin kowace sana’a

Alhaji Abdulhameed Chindo daya ne daga cikin shuwagabannin kasuwar Itoku a Abeokuta, wanda ya ke kasuwanci zinariya. A hirar sa da aminiya, Chindo ya bayyana yadda yadda ya fara sana’a da kuma nasarar da ya samu a halin yanzu. AMINIYA: za ka fada yadda ka samu  kanka  a sana’ar zinariya?Alhaji Chindo: Asali dai agogo da sarka nake […]

Gaskiya da rikon amana ne sirrin kowace sana’a
Gaskiya da rikon amana ne sirrin kowace sana’a

Alhaji Abdulhameed Chindo daya ne daga cikin shuwagabannin kasuwar Itoku a Abeokuta, wanda ya ke kasuwanci zinariya. A hirar sa da aminiya, Chindo ya bayyana yadda yadda ya fara sana’a da kuma nasarar da ya samu a halin yanzu.

AMINIYA: za ka fada yadda ka samu  kanka  a sana’ar zinariya?
Alhaji Chindo: Asali dai agogo da sarka nake sayarwa, ina  zuwa Legas  in sayo in kawo nan  in sayar. Sai na ga sayar da sarkar ta karbe ni, a lokacin wata Hajiya ce kawai ke sayar da zinariya ‘yar saudi, domin a lokacin ba a kawo ta Italy. Sai na yi  sha’awar fara sayar da zinare, nan fa Na fara zuwa kasuwar Wuse, Abuja muna  sayo kaya tare da abokan harkamu na Yaba, Legas. Daga nan muka koma Illori da sayan kaya bisa dalilan tsaron hanya, daga baya sai na yi maigida da yake ba ni kaya daga Dubai. Yanzu ina nan ake kawo min kaya.
AMINIYA: Wace irin nasarori ka samu a kasuwancin ka a halin yanzu?
Alhaji Chindo: Alhamdulillahi na  samu  rufin asiri na yi gidaje a nan da Arewa, na yi  iyali,  sannan ina da yara a kasuwa guda hudu da ke karkashina, na kuma koya wa wadansu sana’ar wadanda a yanzu sun yi  karfi sosai.
AMINIYA: Wane irin kalubale ka fuskanta a wanan sana’ar?
Alhaji Chindo: A baya mun tafka kurakurai da dama wadanda a yanzu muka gyara, sannan an zo runfata an kwashe min kayana bayan  na  cikata da kaya, har  sau  biyu anai min fashi, haka ya sa na shiga matsaloli sosai har sai da abokan arziki suka kawo min dauki aka gyara shago akayi addu’a sannan muka cigaba da harka, ka ga gani har yanzu a cikinta.
AMINIYA: mene ne sirrin sana’ar  Zinariya?
Alhaji Chindo: Sana’a ce  da ribarta ba yawa  sai dai tana  garawa sosai, ko da ribar ba yawa  ana samun  alhairi kwarai, sannan zinariya na da  wani  sirri daya,  ba a kasata kamar  waina, dole ne  a suturtata
AMINIYA: Me ke sa dan kasuwa ya samu aminci da yardar abokan huldarsa?
Alhaji Chindo: Gaskiya ke sa mutum ya samu yarda da cigaba a kasuwanci kowane iri ne, domin duk wanda ya yi harka da kai bai ji dadi ba ba zai dawo ba kuma zai ba ka mummunar shaida, ita kuma harkar kasuwanci ba ta da tabbas, idan yau kana da shi ka iya wayar gari gobe babu, idan kana da gaskiya da amana ko da ba ka da shi sai wani ya tallafa ma ka je ka nemi na abin da za ka ci.