Gaskiya da rikon amana ne sirrin nasarar kamfaninmu – Danfulani

Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarka a takaice? Ni dan asalin Jihar Kano ne a garin Gaya. Ina da shekaru 44 da haihuwa, kuma na yi karatun Muhammdiyya mai zurfi, inda na yi saukar Alkura’ni. Bayan na yi wayo, sai Allah cikin ikonSa Ya hada ni da wani Ubangida na Balarabe mutumin kasar Labanan, inda na […]

Gaskiya da rikon amana ne sirrin nasarar kamfaninmu – Danfulani

Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?

Ni dan asalin Jihar Kano ne a garin Gaya. Ina da shekaru 44 da haihuwa, kuma na yi karatun Muhammdiyya mai zurfi, inda na yi saukar Alkura’ni. Bayan na yi wayo, sai Allah cikin ikonSa Ya hada ni da wani Ubangida na Balarabe mutumin kasar Labanan, inda na yi aiki da shi na wasu shekaru a kamfaninsa na gine-gine. Da ayyukansu suka kare zai koma kasarsu Labanan, sai ya tafi da ni domin ya amince da gaskiya da rikon amanar da na bayyana masa a lokacin da muke aiki a kamfaninsa. A kasar Labanan, na yi ma sa ayyuka da dama, kamar su ajiyar kayansa da dafa ma sa abinci da gudanar da dukkan ayyukan da ake bukatar amana da gaskiya a ciknsu. Ina can ne, sai mahaifa na suka bukacin in dawo gida Najeriya, domin su na ganin kamar na yi musu nisa, ba zan dawo ba. Anan na koyi larabci na kuma hadu da mutane larabawa da yawa. Bayan shekaru uku sai na dawo gida. Da na dawo sai na tsunduma cikin harkar zirga-zirgar ababen hawa, domin cikin ikon Allah, na dawo da rufin asiri mai yawa.

Wani abin takaici ba kasafai al’umma ke fahimtar mutanen kirki masu taimakawa saboda Allah ba, illa nadiran. Irin wadannan mutane suna  nan a boye, sai a wasu lokuta ake saninsu. Kuma masu iya magana na cewa, ‘Babban abin da ya fi muhimmanci a rayuwa shi ne gudumuwar da mutum ya bayar, ba wai yawan shekarun da ya yi a duniya ba.’ Shi ya sanya mutane a garin Kaduna suke ganin mun ciri tuta, kuma mun kafa tarihin da ba kasafai ake kafa irinsa ba, musamman a wannan lokacin da rashin gaskiya da tausayi da kishin al’umma suka mamaye rayuwar yau da kullum.

Aminiya: Da ka dawo daga Labanan, a ina ka zauna?

Na koma garin Bauchi daga baya na koma Kano na zauna na dan wani lokaci, amma da yake abincin yana garin Kaduna, sai na dawo garin Kaduna, na ci gaba da wannan sana’a ta hayar Babura wadda daga baya ta rikide ta zama ta Keke NAPEP. Anan wajibi ne in ambaci wata mata, kodayake ba zan ambaci suna ba, wadda ita ce ta fara ba ni amanar Baburan da nike haya da su, wanda daga baya ta rika ba ni ina ba wadanda na amince da gaskiyarsu da rikon amanarsu. Kuma har yanzu, muna tare da wannan baiwar Allah. Tsakani na da wannan baiwar Allah sai Allah sam barka, da godiyar ban girma. Allah Ya sakamata da hairan.

Aminiya: Ta ya ya za ka bayyana rikidewar sana’ar hayar Babura da Keke NAPEP a bangaren karancin hadurra da samun rufin asiri da sauransu?

E, akwai bambanci matuka. Shi babur kafafu biyu ke gare shi, bai kama kasa ba kamar Keke NAPEP, don haka Keke NAPEP ya fi karancin yin hadari saboda yana da kafafu uku ya kama kasa. Sannan shi babur mutum daya kadai zai iya dauka a lokaci guda, in ya yi yawa mutane biyu. Idan har babur ya dauki mutum uku, to cikin lalura ne, kuma an sabbwa doka. Shi kuma Keke NAPEP yana iya daukar mutane uku, ba tare da matsuwa ba, kuma suna zaune cikin natsuwa, wani lokaci har mutane hudu yakan dauka, kodayake hakan hukuma na tsawatar wa akai. Don haka, a ra’ayina Keke NAPEP ya dara babur, domin hatta abin da mutum zai samu a wuni guda, ya fi abinda babur kan samu. Don haka, canjin da aka samu daga sana’ar babur zuwa Keke NAPEP wani ci gaba ne aka samu mai ma’ana wanda ya kawo sauyi a harkar sana’ar baki daya. Kodayake hakan ya kawo cikas ga wasu abokan sana’armu masu Babura, amma dai an samu ci gaba, kuma muna yi musu fatan alheri da addu’ar Allah Ya taimaka musu su samu Kekunan da za su ci gaba.

Aminiya: Wace irin nasara ka samu bangaren rufin asiri da samar da ayyukan yi ga matasa?

Ai wannan ba a magana. Da lokacin da na fara wannan sana’ar ya zuwa yanzu, na samu rufin asirin da ba zan iya misalta shi ba. Sannan a halin yanzu, akwai kekunan NAPEP daruruwa wadanda matasa da magidanta ke aiki da su a Jihar Kaduna da Kano da Katsina wasu kuma a birnin tarayya Abuja. A kalla akwai matasa sama da 250 dake son in ba su kekunan NAPEP don su yi aiki su samu rufin asiri. Akan haka ne da na ga al’amarin yana bunkasa, sai na yi rijistar kamfanin  nan. Wadannan matasan dake ayyuka a karkashin wannan kamfanin, mafi yawancinsu sun yi auratayya da sayen filaye da gidajen zama yanzu haka sun zama mutanen kirki masu abin-yi a cikin al’umma. Don haka, a kullum muna samun sakonnin godiya da Allah da sam barka da jinjinar ban-girma a sakamakon hakan.

Aminiya: Na ga dukkan kekunanka na Kamfanin Bajaj ne. Ko akwai wata alaka da kamfanin ne?

Gaskiya ne, saboda yawan Kekunan da nike saye daga wajen dilolin Bajaj, har sai da Babban Kamfanin dake kasar Indiya suka ba ni lambar yabo da sanya ni cikin manyan dilolinsa a kasar nan, musamman a Jihar Kaduna. Saboda haka ne, a shekarar 2016 Kamfanin ya turo injiniyoyinsa da kanikawansa suka zo yadina dake NDA Bus stop Kaduna, ya horadda da kanikawan Keke NAPEP Bajaj kyauta, ba tare da ko sisin kobo ba. Haka suka sake dawowa a shekarar 2017 ma sun sake dawowa inda suka sake horadda wasu kanikawan kyauta, a dai yadi na dake NDA. Sannan a halin yanzu, wannan kamfani yana da alaka da hulda mai kyau da babban kamfanin na Bajaj dake kasar Indiya, inda ni kan aika kai-tsaye in yi odar Kekunan Bajaj ba tare da wani shamaki ba. Don haka, ina da alaka da Babban Kamfanin, kuma sun san da zamanmu a wannan jihar, saura kawai gwamnatin Jihar Kaduna ta gane gudumuwar da muke bayarwa ga samar da ayyukan yi ga matasa da magance zaman banza a tsakaninsu, ta hada hannu da mu domin samun ci gaba dawwamamme.

Aminiya:  Ko wadanne matsaloli ne ka taba fuskanta a wannan sana’ar?

Babu wata matsalar da nike fuskanta illa ta halayen ‘yan adam. Idan ka taimaki mutum, maimakon ya rike taimakon, amma sai ya kuma saka maka da sharri. Wannan shi ne babbar matsalar da nike samu. Domin idan da mutanen da muka taimaka wa, sun rike wannan taimakon sun rike dukiyar jama’a, da ba za a samu wata mishkila ba. Amma sai ka samu akasin haka. Wannan shi ne. Ina kira ga duk wanda wata mu’amala ta hada mu, da ya rike amana da sanya gaskiya da rikon amana da cika alkawali. Amma da yake don Allah ka ke yi, ko an samu akasi babu wata damuwa. A kullum, sai gaba-gaba muke yi a wannan kamfani.

Aminiya: Me za ka ce dangane da gwamnati, musamman a sashen Kafa Hukumar kare hadurra da rage hadurran hanya ta KASTELEA da gyaran hanyoyin Jihar Kaduna?

E, wannan abin yabo ne matuka. Lalle Gwamna Nasiru El-rufai ya taka rawar gani da ya habbaka wannan hukuma ta KASTELEA, wadda ke yin ayyukan dake rage cunkoso da hadurran ababen hawa. Wannan hukuma abin yabo ce. Sannan a ayyukan samar da ababen jin dadin rayuwa irinsu hanoyi da harkar ilmi da kiwon lafiya, Gwamnatin El-rufai tana namijin kokari sosai. A bangaren hanyoyin inda sana’armu ta dogara akai, gwamnatin na gyarawa da samar da hanyoyi masu inganci bakin gwargwado. Akwai hanyoyi sama da 700 manya da kanana a ko’ina a fadin jihar Kaduna. Wannan abin yabo ne da godiya ga wannan gwamnatin. Haka a sashen ilmi, ana ta gyaran makarantu da daukar malamai da gyaran asibitoci da kakkafa kamafanoni irinsu Olam Feeds dake babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da gyaran matatun ruwan sha irinsu ruwan Zaria. Wani abin yabon kuwa shi ne tabbatar da zaman lafiya musamman a yankin Kudancin Kaduna da dai sauran ayyukan alheri. Don haka, muna fatan alheri ga wannan gwamnatin da yi ma ta addau’a.

Aminiya: A matsayinka na wanda ke samar da ayyukan yi ga matasa a Jihar Kaduna, ta yaya gwamnati za ta iya taimaka ma ka?

Akwai hanyoyi da dama wanda ita gwamnatin za ta iya taimakawa, amma ba zan so in fade su ba, domin ina ganin kamar roko ne, kuma a tsarin rayuwata, ban san in cika roko da zura jiki akan al’amari. Tun da dai mun yi rijista da gwamnati, kuma muna samar da ayyukan yi ga matasa, ita gwamnatin ta san da zamanmu da ayyukan da muke yi. A gani na, ta san inda ya kamata ta shigo ta taimaka mana, ba sai mun zura jiki ba, mun ce muna son kaza da kaza ba. Abin da kawai zan ce ko kiran da zan yi shi ne duk wata hanyar da za ta tallafa wa wannan sana’a ta mu, to muna bukatar gwamnatin ta shigo ta samar da yanayin da wannan sana’ar ta mu za ta bunkasa don mu ma mu ci gaba da samar da ayyukan yi ga matasa fiye da haka.

Aminiya: Wane kira zaka yi ga matasa, musamman masu wannan sana’ar ko wadanda ke son su shigo domin samun rufin asiri?

Kiran da zan yi shi ne su rike amana da aikata gaskiya da cika alkawalin da suka dauka, domin alkawali kaya ne, kuma abin tambaya ne a wurin Allah. Ga dukkan wanda ke son ya samu nasara, wadannan halaye su ne tushe, kuma ginshikan nasara ba ma sana’ar zirga-zirgar ababen hawa ba, har ma al’amurran rayuwa baki daya. Kuma rike wadannan halayen su ne tushen nasara da wasu ke ganin na samu. Rashinsu shi ne ke kawo rashin nasara a dukkan ala’amari. Na gode. 

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno