Gaskiya dokin karfe

Mutane da yawa ba su yi mamakin yadda Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta daga kara gaban tarkon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar, SIECOM ta kafa ba  game da tsayar da ranar da za a yi zaben shugabanni da kuma kansilolin kananan hukumomi ashirin da uku da ke fadin jihar, domin tun can […]

Gaskiya dokin karfe

Mutane da yawa ba su yi mamakin yadda Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta daga kara gaban tarkon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar, SIECOM ta kafa ba  game da tsayar da ranar da za a yi zaben shugabanni da kuma kansilolin kananan hukumomi ashirin da uku da ke fadin jihar, domin tun can da farko sun san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Rashin gudanar da zaben kananan hukumomi a jiha kamar Kaduna, wacce talakawan cikinta kawunansu suka waye, idanuwansu suka bubbude, suka kuma san hakkokinsu abu ne wanda ya dada su da kasa ainun, ganin cewa wajibi ne a ba su damar yin amfani da ‘yancinsu da kundin tsarin mulki ya fayyace na zaben wadanda suke so su jagoranci al’amuransu a kananan hukumominsu daidai da yadda suka yi  haka a zabubbukan ‘yan majalisun jiha da na tarayya da kuma gwamna har ma da na shugaban kasa.  Talakawa dai sun san cewa babu wani dalilin da zai jinkirta wannan zabe, kuma sun ki su amince da yadda aka yi ta sabunta musu shugabannin da ake ta kakaba musu, abin da suka tabbatar haramun ne, domin babu wanda zai shugabanci karamar hukuma sai wanda jama’a suka taru suka ba iznin yin haka da zunzurutun kuri’unsu.

Sakamakon yadda Gwamna Nasiru el-Rufa’i ke ta canja shugabannin kananan nhukumomin da yake ta nannadawa kamar yadda yake kwabe shakwararsa cikin sauki ba tare da damuwa da korafin jama’a na cewa an tauye musu hakkinsu ba game da haka, sai wasu da abin ya fi tunzurawa suka sheka kotu don neman hakkinsu, watau a tilasta wa gwamna gudanar da zaben kananan hukumomi. Babbar Kotun Jihar Kaduna ta share wa musu kuka game da haka hawaye, inda ta umurci gwamna da ya dauki matakan gaggawa don tsara zaben da zai ba talakawa damar darje wanda suke so ya shugabance su.  To amma me ya faru, an yi zaben? Ina fa aka yi, hasali ma kara jan kafa aka yi, aka yi ta  kago wasu hujjojin da ba su gamsar da jama’a ana kawowa dangane da gazawar da ake yi na gudanar da zaben.

daya daga cikin dalilan da aka gabatar game da haka shi ne wai za a yi zaben ne da na’ura irin ta zamani wacce ba a taba yin amfani da irinta ba a kasar nan don a yi zaben da zai sha bamban da na sauran jihohi wajen inganci da kuma gamsar da jama’a. An ce an rigaya an yi sautun wadancan na’urorin har guda dubu shida daga kasar Brazil, sun kuma iso, har an yi wa kwamishinoni da gwamna gwajin yadda za a sarrafa su, amma babu ya ce ya taba ganinsu  ban da su kansu da kuma wasu tsirarun ‘yan jaridar da aka yi wa gwajin wata na’urar, ko kuma ga yadda za a sarrafa su, kuma duk da haka nan an cika duniya da yare cewa da su ne za a yi zaben. Baicin haka nan kuma gwamnati ba ta samar da  kudin da za a bai wa hukumar zaben don sayen wadancan na’urorin ba da sauran kayayyakin aikin da take bukata wadanda aka kiyasta sun kai dubban miliyoyin Nairori.

A takaice dai kowa ya san cewa dogon jinkirin da ake samu a Jihar Kaduna game da gudanar da zaben kananan hukumomi bai rasa nasaba da batun kudin da gwamnati ba ta da su, ba ta kuma fito fili ta yi wa jama’a bayani game da haka ba, sa’annan kuma ta ki ta fayyace dalilan da suka hana ta fitar da kudin. Wannan ne ya sa ‘yan adawa da sauran jama’a, musamman ma ‘yan takarar da suka kosa su samu damar  hayewa kujerun da za su yi wa  mutanensu ayyukan alheri  suka yi ta yin korafi  suna nuna alamun cewa gwamnati dai ba ta son  yin zaben kananan hukumomi ne, kuma tana dukkan nuku-nukun da ya kamata don kada a yi.

To shi ne hukumar zaben ta ga zai yi kyau ta  yar da kwallon mangwaro ta huta da kuda, saboda haka nan  sai kwatsam aka ji ta bayyana jadawalin gudanar da zabe na tsawon watanni uku, daga ranar 29 ga watan Satumba zuwa ranar talatin ga watan Disamba da kuma matakai daki-daki don kaiwa ga haka. Ai rufe bakinta ke da wuya, sai ga Shugaban Kwamitin Shari’a na majalisar Dokokin Jihar Kaduna na jan kunnen hukumar zaben da kada ta kuskura ta gudanar da zaben, domin kuwa majalisa ba ta kammala aikinta ba kan dokar gudanar da zaben balle gwamna ya sanya mata hannu har a yi amfani da ita wajen tsara matakai da ka’idojin gudanar da zaben

Dangane da haka ne Shugabar hukuma, Dokta Saratu Dikko ta ce ta dakatar da dukkan shirye-shiryen da take yi don gudanar da zaben, sa’anan kuma bayan ta tattauna da gwamna da kuma manyan kusoshin gwamnatinsa sai ta bayyana cewa an dage zaben har sai illa masha-Allahu, amma kuma  wai ba a ce  ba za a yi ne ba, sai  abin da hali ya yi nan gaba. Wannan matsayi da Dokta Saratu Dikko ta dauka ya kara tabbatar da ra’ayin mafiya rinjayen jama’a da ke cewa ba zaben za a yi ba, ana so ne a yi yaudara a  kuma yi wasa da hankulan jama’a har sai lokaci ya kure.

To amma abin da ban mamaki a ce daga cikin jihohi talatin da shida na fadin tarayyar Najeriya inda aka sha yin zabubbukan kananan hukumomi fiye da  shurin masaki, ba a taba samun wata hukumar da ta yi gaban kanta ba wajen tsara zabe ba tare da dokokin gudanar da zaben da majalisa ta samar ba. Haka nan kuma ba a taba samun majalisar da ta yi jinkiri wajen samar da dokokin gudanar da zabe kamar ta Kaduna ba, duk kuwa da irin danyen ganyen da take dasawa da Gwamna el-Rufa’i, tun da dai mutum ba zai yi abota da dan biri ba sa’anan kuma sandarsa ta makale a sama. A yanzu ana iya cewa hadin baki ne aka yi da majalisar dokokin Jihar Kaduna game da  jinkirta fitar da dokokin zaben, ko kuwa ita gwamnatin ce da kanta ke neman hana ruwa gudu game da zaben kananan hukumomin domin tana ganin cewa idan har an yi zaben za ta kwashi kashinta a hannu? To idan har ba ta bari an yi zaben ba don kar ta sha kashi, tana tsammani barin kashi a cikinta zai yi mata maganin yunwa ne? Ko ba jima ko ba dade dai sai an yi zaben kananan hukumomi, kuma ci gaba da jinkirta shi zai kara haddasa matsaloli ne irin wadanda aka nemi guje musu ta hanyar jinkirta shi. To wai shin  nan hukumar zabe tana tsammani za ta iya  bugun kirji, ta nemi gudanar da zaben duk kuwa da cewa tana sane da wadancan matsalolin da ba za su bari ta kai ga nasara ba? Yanzu dai abin da zai fi shi ne Gwamna Nasir ya hau dokin karfe, ya fito fili ya fayyace wa  jama’a gaskiya game da halin da ake ciki da zaben kananan hukumomi. Gaskiyar ce kawai madogaronsa game da haka.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos