‘Gaskiya ita ce kashin bayan samun duk wani alheri’

Wani matashi dan asalin garin Wauru cikin karamar Hukumar Gada, Jihar Sakkwato, Surajo Abdulkadiri mai sana’ar sayar da dabino kuma a lokaci guda yana gyaran wayoyin salula, ya ce gaskiya ita ce kashin bayan samun duk wani alheri.Kamar yadda ya fada a zantawarsa da wakilin Aminiya a garin Benin a kwanan baya: “Hakika na lura […]

‘Gaskiya ita ce kashin bayan samun duk wani alheri’
‘Gaskiya ita ce kashin bayan samun duk wani alheri’

Wani matashi dan asalin garin Wauru cikin karamar Hukumar Gada, Jihar Sakkwato, Surajo Abdulkadiri mai sana’ar sayar da dabino kuma a lokaci guda yana gyaran wayoyin salula, ya ce gaskiya ita ce kashin bayan samun duk wani alheri.
Kamar yadda ya fada a zantawarsa da wakilin Aminiya a garin Benin a kwanan baya: “Hakika na lura cewa gaskiya ita ce kasahin bayan tafiyar da harkokin komai na sana’a da mutun yake yi. Wannan za ta sa mutane yin mu’amala da kai cikin yarda da mutunci. Don haka, kowa ya rike sana’arsa da gaskiya zai ga haske na alheri a rayuwarsa.” Inji shi.
Sannan ya ce ya kamata mutane su gane ba wai sai da wata babbar sana’a mai cakude da ha’inci da zamba ake samun biyan bukata ba, domin da dama rashin gaskiya yana jefa wasu mutane masu manyan sana’a cikin matsala, har ya kai sana’ar ta rushe.Matashin sai ya ce: “Don haka ka gani ina da kananan sana’a guda biyu a gabana. Na farko ga wannan dabino ina sayar da shi kullum babu fasawa kuma ina samun riba gwargwado. A dayan wannan teburin kuma ga wayoyin salula na mutane da suke kawo mani ina yi musu gyaransu kuma ban taba bari wayar mutum ta bata a wurina ba, don haka a bangaren wannan gyaran sai in ce Alhamdu lillahi. Ban taba in kwance waya ta gagare ni hadawa ba. Don haka ba ni da wata matsala tsakanina da abokan huldana masu kawo man gyara, tun da da na fara aiki kawo yau.”
Ya ce ya samu ci gaba a wannan sana’a guda biyu, inda ya samu babban rufin asiri, domin da su yake taimakon iyaye da ’yan uwa idan wata bukatar ta taso ba sai ya je wata maula ba ko kashe murya a gaban kofar wani ba. “Don haka ina kira da babbbar murya ga ’yan uwana masu kananan sana’a, har da masu manyan sana’ar da cewa mu rike gaskiya, mu nisanta kanmu daga zamba ko ha’inci cikin sana’o’inmu. Idan muka amsa wannan kiran, to wannan zai sa abokan huldanmu su mutunta mu tare da samun kyakyawar sakayya wurin Ubangiji.” Inji shi.