Gaskiyar Buhari ce ta sa ya gagari abokan adawarsa – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce gaskiya da rikon amanar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, suka sa ya gagari abokan adawarsa. Sheikh Jingir, ya bayyana haka ne lokacin da yake bude wani sabon masallacin Juma’a da Makarantar Islamiyya da wani dan […]

Gaskiyar Buhari ce ta sa ya gagari abokan adawarsa – Sheikh Jingir
Gaskiyar Buhari ce ta sa ya gagari abokan adawarsa – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce gaskiya da rikon amanar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, suka sa ya gagari abokan adawarsa. Sheikh Jingir, ya bayyana haka ne lokacin da yake bude wani sabon masallacin Juma’a da Makarantar Islamiyya da wani dan kasuwa, Alhaji Abubakar Sulaiman ya gina kuma ya bai wa kungiyar, a Unguwar Randar Ruwa Rikkos da ke Jos, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya ce Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, wanda daga hawansa mulkin Najeriya zuwa yanzu, ya yi abubuwa masu yawa na ci gaba a kasar nan.

Ya ce baya ga samar da tsaro da Shugaba Buhari ya yi, ya bunkasa harkokin noma kuma yana kokarin dora kasar nan kan turba tagari, tare da farfado da harkokin masana’antu.

“Ko a ’yan kwanakin nan Buhari ya je  kasar China, ya ce su zo su  kafa masa’ana’antu a Najeriya. Wannan hali na Buhari ya jawo masa farin jini a ciki da wajen Najeriya. Mutum ba zai san farin jinin Buhari ba, sai ya je kasashen waje”, inji shi.

Sheikh Jingir ya yi kira ga al’ummar Najeriya, su ji tsoron Allah su rike gaskiya. Ya ce   idan muka rike gaskiya za mu samu nasara a duniya da Lahira, kuma mu samu ci gaba a Najeriya.

Sheikh Jingir ya ce saboda gaskiyar da  kungiyar Izala ta rike ne, ya sa ta samu nasarar  karantar da dalibai sama  da miliyan 6 a makarantun kungiyar  na Najeriya da kasashen makwabta. 

Ya taya Alhaji Abubakar Sulaiman murnar  gina masallacin da makarantar, inda ya ce Allah ne kadai Ya san yawan mutanen da za su rika yin Sallah a masallacin da dimbin mutanen da za a karantar a makarantar. Sai ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi koyi da wannan bawan Allah.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa