Gaskiyar magana kan batun ‘rusa’ sashen Masallacin Abuja

Tarihin kafa Masallacin Abuja yana hade ne da kirkiro wannan birni na Tarayya.

Gaskiyar magana kan batun ‘rusa’ sashen Masallacin Abuja

Masallacin Kasa da ke Abuja

A makon jiya ne aka yi ta yayata labarin yunkurin rusa wani sashe na Masallacin Kasa da ke Abuja inda aka danganta hakan ga Ministan Birnin Nyesom Wike.

Aminiya ta zanta da Dokta Muhammad Kabir Adam, daya daga cikin limaman masallacin, inda ya yi bayani hakikanin lamarin.

Yaya za ka bayyana tarihin kafa Masallacin Abuja?

Tarihin kafa Masallacin Abuja yana hade ne da kirkiro wannan birni na Tarayya.

Marigayi tsohon Shugaban Kasa Janar Murtala Mohammed (Allah Ya ji kansa), shi ne ya kirkiro Abuja kamar yadda aka sani.

Bayan rasuwarsa sai gwamnatin da ta biyo baya a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kasa Janar Olusegun Obasanjo ta fara tunanin yadda za a samar da masallaci na kasa da kuma coci na kasa a Abuja.

To a lokacin tsohon Shugaban Kasa marigayi Shehu Shagari (Allah Ya ji kansa) ne nake jin aka ba da fulotin masallacin ga Musulmi da kuma na Cocin Kasa ga Kiristoci.

An zauna, an yi shawara a tsakanin bangarorin biyu, Musulmi suka dauki nan, Kiristoci suka dauki na cocin da ke kusa da Babban Bankin Nijeriya, bisa ga fahimtar juna.

Bayan nan sai gwamnatin Shagari ta ba da Naira miliyan goma-goma ga bangarorin biyu a matsayin gudunmawarta ta fara aikin gini, amma ba da niyyar ita ce za ta yi aikin ginin ba.

A 1982 sai marigayi Sarkin Musulmi, Abubakar na Uku ya kafa kwamitin aikin ginin masallacin a karkashin shugabancin marigayi Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa, (Allah Ya gafarta musu baki daya).

An dora wa kwamitin nauyin nemo taimakon kudin aikin da kuma gina masallacin baki daya.

Haka ya jagoranci fara aikin, ba a kuma tsaya ba har sai da aka kare aikin dungurugum.

A lokacin Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida, an gudanar da gidauniyar neman taimako don ci gaban aikin masallacin, inda ya zo wajen taron da kansa, ya ba da gudunmawar Gwamnatin Tarayya ta Naira miliyan hamsin.

Ya kuma ba da taimakon ne ta hannun Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya tun da su ne masu masallacin, shi ya sa shugabanta, wato Mai alfarma Sarkin Musulmi shi ke nada Kwamitin Gudanarwar Masallacin.

Alhamdulillahi aikin farko da aka fara yi a masallacin bayan an kammala shi, shi ne taron da aka kira na Islam in Africa Conference, wanda ya gudana a Babban Dakin Taro na Masallacin a 1988.

A 1991 a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Janar Babangida bayan ya dawo da Birnin Tarayya daga Legas zuwa nan Abuja a ranar Laraba, Juma’a na zuwa sai aka yi Sallar Juma’a tare da shi, kuma a lokacin ne aka bude masallacin.

Kuma tun a wancan lokaci ba a taba rufe shi ba, sai da matsalar Kwarona ta zo.

Wacce gudunmawa masallacin ya samu bayan Gwamnatin Obasanjo ta karbi masallacin da kuma cocin a masayin kadarorin kasa da take ji da su?

Hakika wuraren biyun sun samu gudunmawar gwamnati kuma a dalilin haka daga bara zuwa bana an yi ta gudanar da ayyukan gyara a masallacin da kuma cocin, wanda Ma’aikatar Birnin Tarayya ta rika aiwatarwa.

An yi ta aikin kwaskwarima wanda ya hada da magance matsalar yoyon ruwan sama da aka yi ta fama da shi.

Ka ga duk yawan ruwa da aka yi a bana, ba a fuskanci matsalar yoyon ba.

Sai ga labari a makon jiya cewa sabon Ministan Abuja Nyesom Wike zai rusa bangaren masallacin.

Mene ne gaskiyar batun?

Zan iya cewa wannan shaci-fadi ne ko soki burutsu, saboda babu wannan maganar.

Hakikanin abin da ya faru shi ne, Shugaban Kwamitin Masallacin, Mai martaba Esu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ya jagoranci Hukumar Gudanarwar Masallacin zuwa ofishin sabon Ministan Abuja don yi masa barka da zuwa.

A matsayinmu na Musulmi muna girmama shugabanci kuma wannan shi ya kai mu.

Dalili na biyu kuma na ziyarar shi ne don gabatar masa da korafi a kan sanarwa da ma’aikatarsa ta fitar na kwace daukacin fulotan da gwamnati ta bayar a baya aka gaza gina su.

Ya ba da wa’adin wata uku na a aiwatar da aiki a wuraren ko a kwace su.

To fulotai biyu mallakin wannan masallaci da suka hada da wanda yake tsakaninmu da Cibiyar Shehu Musa ’Yar’aduwa da kuma wanda ya faro daga bayan ginin masaukin baki na Sheraton zuwa masallacin da ke daura da shi wanda da ma shi ne kamfanin da ya gina masallaci ya kafa sansaninsa a wajen, suna cikin wadanda aka buga a jaridu kan wa’adin kwacewa da Ministan ya sanar.

Mun gabatar masa da korafi cewa ai ya san cewa mu masallaci ba wani kudi muke da shi ba.

Mun kuma sanar da shi inda aka tsaya kan batun aiki a filin da ke daura da masallacin, inda ya nuna gamsuwarsa.

Shi kuma daya filin da ke tsakaninmu da Cibiyar Shehu Musa ’Yar’aduwa, mun sanar da shi cewa a lokacin da muka bukaci Hukumar Birnin Tarayya ta ba mu takardar amincewar fara yin aiki, sai ta sanar da mu cewa, akwai aikin titi da zai ratsa ta bangaren filin.

Saboda haka dole sai an fitar da filin da aikin zai shafa tukuna. To mun sanar da shi cewa wannan shi ne abin da ya haifar da jinkirin fara aiki a filin.

Mun kuma nemi wata alfarma ta musamman a kan wannan filin daga wajen sabon Ministan.

Na farko kan a cire fili da zai rage, sannan na biyu a maye mana gurbin fulotin da aikin zai shafa.

Ai ka ga babu batun rusa masallaci a lamarin. Wadannan su ne bukatun da muka gabatar ga Ministan kuma ya amince da su.

A nan take ya kira Hukumar Raya Birnin Abuja, (FCDA) ya ba su umarnin su yi aiki a kai tare da mika masa rahotonsu a cikin awa 24, saboda muhimmacin lamarin.

Sun kuma gabatar masa da rahotonsu a cikin wannan lokaci, har ya duba, ya yi nasa aikin tare da mika takardar ga mataki na gaba.

Mun kuma sanar da shi cewa, a lokacin tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ya mayar da masallacin da cocin a matsayin wurare biyu masu muhimmaci ga gwamnati, inda Ministan ya nuna gamsuwarsa da hakan.

Wannan shi ne hakikanin abin da ya faru, don haka babu batun rusa wani bangare na masallacin. Soboda haka, babu wannan magana, kuma ba musan ta inda wannan magana ta faro ba.

Me Hukumar Masallacin take son yi da filayen biyu?

Fuloti da ke daura da masallaci muna son mu gina masaukin baki ne, saboda idan ka duba a daukacin wannan birni masaukin baki wanda za a kira shi na Musulunci guda daya ne kawai, wato wanda yake Unguwar Life Camp a nan Abuja.

Ka ga ke nan idan aka kara wani ai zai amfani al’umma.

Shi kuma fuloti na biyun da ke tsakaninmu da Cibiyar Shehu Musa ’Yar’aduwa abin da muka tsara yi shi ne, kafa wurin wasa da nishadi na yara don amfanin al’umma.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja