Gattuso ya koma Lazio a matsayin sabon mai horaswa
Gattuso ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu, inda zai riƙa karɓar albashin yuro miliyan 1.5 a duk shekara.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Lazio ta sanar da ɗaukar Gennaro Gattuso a matsayin sabon mai horas da ’yan wasanta, watanni kusan uku bayan ƙarewar taƙaitaccen wa’adinsa a matsayin kocin tawagar ƙasar Italiya wadda ya raba gari da ita bayan gaza samun tikitin zuwa Gasar Kofin Duniya.
Cikin wata sanarwa da Lazio ta fitar a ranar Talata, ta ce: “S.S. Lazio S.p.A. na sanar da naɗa Mista Gennaro Gattuso a matsayin shugaban masu horas da tawagar farko ta ƙungiyar.”
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Italiya sun ce Gattuso ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu, inda zai riƙa karɓar albashin yuro miliyan 1.5 a duk shekara.
- Sojoji sun ceto mutum 47 daga hannun ’yan ta’adda a Borno
- Mazauna wata unguwa na bore kan buɗe gidan ’yan fim a Kano
Gattuso ya koma aikin horaswa a gasar Serie A, inda ya yi fice a matsayinsa na ɗan wasa tare da AC Milan, ƙungiyar da ya shafe shekara 13 yana bugawa, har ya lashe kofin Serie A sau biyu da kuma Gasar Zakarun Turai a shekarun 2003 da 2007.
Ya maye gurbin Maurizio Sarri, wanda ya kawo ƙarshen kwantiraginsa da Lazio a ƙarshen watan da ya gabata bayan kakar wasa mai cike da takaici, wadda ƙungiyar ta kammala a matsayi na tara a teburin Serie A, sannan ta sha kashi a wasan ƙarshe na Kofin Italiya a hannun Inter Milan.
Gattuso mai shekara 48 zai fuskanci ƙalubale mai girma, kasancewar magoya bayan Lazio sun shafe mafi yawan kakar wasan da ta gabata suna ƙaurace wa wasanni domin nuna rashin jin daɗinsu da shugabancin mai ƙungiyar na tsawon lokaci, Claudio Lotito.
Sai dai har yanzu Gattuso bai samu irin nasarorin da ya samu a matsayinsa na ɗan wasa ba, inda Kofin Italiya da ya lashe tare da Napoli a shekarar 2020 shi ne babbar nasararsa a fagen horaswa.
A watan Yunin bara ne ya maye gurbin Luciano Spalletti a matsayin kocin tawagar ƙasar Italiya, inda ya yi nasara a wasanni shida cikin bakwai da ya jagoranta.
Sai dai wasansa na ƙarshe ya kasance mai raɗaɗi, bayan da Bosnia-Herzegovina ta doke Italiya a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan neman gurbin shiga Kofin Duniya da aka tashi 1-1 a Zenica.
Wannan rashin nasarar ya sa Italiya ta kasa samun gurbin shiga Gasar Kofin Duniya karo na uku a jere, inda a yanzu ta kasance cikin masu kallo a gasar da ake gudanarwa a Amurka, Kanada da Mexico.