Gausiyya ba sabon abu ba ne a darikar Tijjaniya – Sadisu Abubakar

Kwamnakin baya ne gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa akwai wata kungiyar addnin musulunci mai zazzafar akida mai suna Gausiyya a yankin karamar hukumar  Makarfi, a tattaunawar da Aminiya ta yi da shugaban kungiyar a Makarfi Malam Sadisu Abubakar Makarfi ya karyata wannan zargin, inda ya ce su  musulmi ne ‘yan darikar […]

Gausiyya ba sabon abu ba ne a darikar Tijjaniya – Sadisu Abubakar
Gausiyya ba sabon abu ba ne a darikar Tijjaniya – Sadisu Abubakar

Kwamnakin baya ne gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa akwai wata kungiyar addnin musulunci mai zazzafar akida mai suna Gausiyya a yankin karamar hukumar  Makarfi, a tattaunawar da Aminiya ta yi da shugaban kungiyar a Makarfi Malam Sadisu Abubakar Makarfi ya karyata wannan zargin, inda ya ce su  musulmi ne ‘yan darikar Tijjaniya, mabiya mazhabar Imamu Malik. Ga yadda hirar ta kasance:

Sadisu Abubakar Makarfi, Shugaban Gausiyya a MaqarfiAminiya- Kwanakin baya Gwamnan Jahar Kaduna Ya bayyana cewa akwai wata kungiyar  Gausiyya da ka iya zama barazana ga tsaron kasa, yaya kuka  ji wannan batu?
Ni ina daya daga cikin Jagorori na Sabon Gausi da ke a garin Makarfi. A lokacin da muka saurari wannan hira ko bayani na gwamna sai muka ji kamar ya shafe mu ta barayi daya, amma ta barayoyi uku sai muka ga  bai shafe mu ba. Magana ta farko da ta shafe mu da ya ce sunan kungiyar Gausiyya. Na biyu kuma da muke ganin bai shafe mu ba shi ne inda ya ce suna sallar azahar karfe 11 na safe, wanda mu kuma duk wanda ya sanmu ya san ba ma sallah karfe goma sha daya. Sannan kuma maganar da muke ganin ba ta shafe mu ba ita ce,  ya ce wai malamin yana da malami a Barnawa kuma an yi zama da malamin nasa, wanda ya kuma ce shi ba shi ya koya masa wannan akida da yake kai ba.Wannan ma sai muka ji bai shafe mu ba.  Dalilin ke nan da ya sa muke ganin abin kamar ya shafe mu ko bai shafe mu ba. Domin maganar yin sallah karfe 11, duk wanda ya sanmu ko yake da labarinmu  ya san ba haka ba ne.

Aminiya: Gwamnan ya bayyana kungiyarku a matsayin wata sabuwar kungiyar addini ce mai zazzafar akida.
Game da wannan bayanin za mu ce kusan mu ba mu fahinci bayanin a haka ba, ba don komai ba kuwa saboda mu ba kungiya ba ce , mu musulmi ne ‘yan darikar Tijjaniya, muna bin mazhabar Imamu Malik, kuma Gausiyya ba sabuwar  abu ba ce, domin ta samu asali cikin addini tun gabanin bayyanar Shaihunmu, Malanmu Shehu Tijjani. Bayan shaihu Tijjani an samu Agawasi da yawa, kamar su Shehu Aliyu Tawasini, irin su Shehu Umaru Kuti, irin su Shehu Ibrahim Inyass, wanda shi jama’a suka fi sani a matsayin Gausi, wannan Shehu Ismail shi ne wanda ya khalifanci Shehu Ibrahim bayan wucewar karnin Shehu Ibrahim din. Saboda haka wannan bai zama sabon addini ba.

Aminiya: Yanzu da ake ganin kun fito da wata zazzafar akida, me kuke son gwamna da sauran jama’a su sani dangane da akidarku?
Abin da muke son gwamna da sauran jama’a su sani dangane da mu shi ne, kofarmu a bude take, duk wanda yake son ya ga abin  da muke yi zai iya zuwa. Duk wanda yake son ya yi hira da mu zai iya zuwa ya tambaye mu kuma ba mu da wani abu da yake a boye. Duk abin da muke yi a bayyane muke yinsa, kuma duk abin da muke yi muna yinsa na a bisa hujjoji na shari’ar musulunci, a bisa Kur’ani da Hadisi 

Aminiya:  Wane kira kake da shi ga al’umma dangane da akidarku!
Kiran da zan yi wa al’umma shi ne, kamar yadda bayanai suka nuna a bisa Kur’ani, adalci shi ne a yi bincike kafin zartar da hukunci, kuma a zauna da wanda abu ya shafa, saboda dalilin zama da wanda abin ya shafa ne za a gane ainihin mai yake yi, idan har akwai kuskure a cikin abin da ya ke yi sai a fahimtar da shi.