Gawa 3 aka gano tare da ta Nabeeha

Har da wata ’yar sakandare mai shekaru 13, Folorunsho Ariyo, wadda aka sace tare da mahaifiyarta da ’yan uwanta uku

Gawa 3 aka gano tare da ta Nabeeha

Gawa

’Yan bindiga sun kashe karin mutane daga cikin mutane 10 da suka sace a Rukunin Gidaje na Sagwari da ka Abuja ranar Lahadi 7 ga watan nan na Janairu.

Daga cikin karin ’yan rukunin gidajen da aka kashe har da wata ’yar sakandare mai shekaru 13, Folorunsho Ariyo, wadda aka sace tare da mahaifiyarta da ’yan uwanta uku.

Mazauna rukunin gidajen sun ce masu gurkuwa da mutanen sun yi wa kwarin mutum biyu kisan gilla ne sakamakon jinkirin ba su kudin fansar da suka nema, da nafin matsa wa ’yan uwansu su biya.

Wasu shaidu sun ce bayan kashe karin mutane biyun, masu garkuwar sun kara kudin da suke nema kan kowane mutum zuwa Naira miliyan 100 daga miliyan N60 da suka nema da farko.

Mazauna yankin na shirin gudanar da zanga-zanga a yau Talata domin matsa wa gwamnati ta kawo musu dauki wajen ceto ragowar wadanda ke hannun masu garkuwar.

Da alama dai an kashe su ne tare Nabeeha Al-Kadriyar, dalibar aji biyar a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, wadda ita kuma aka sace tare da mahafinta da ’yan uwanta biyar a wani harin na daban a Abujan a ranar 9 ga wata.

Labarin kisan Folorunsho Ariyo, kamar na kisan Nabeeha Al-Al-Kadriyar, ya jawo kiraye-kiraye a soshiyal midiya inda ake ta n kawo karshen matsalar tsaro a Abuja.

Masu garkuwar sun sako mahaifin Nabeeha ranar Talata da cewa ya kawo kudin fansan ’ya’yansa Naira miliyan 60 kafin ranar Juma’a, amma suka kashe Nabeeha saboda miliyan 30 aka iya hadawa zuwa ranar, sannan suka kara kudin zuwa miliyan 100.

Wani kawun Nabeeha ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa a lokacin da suka je daukar gawarta sun ga karin gawarwaki uku – mata biyu da namji daya.

Sai dai zuwa yanzu babu bayani game da namijin da daya macen.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun jefar da gawarwakinsu su hudu ne a kusa da wani tsohon shingen binciken ababen hawan sojoji a kan hanyar Bwari zuwa Jere da ke Karamar Hukumar Kagarko da ke Jihar Kaduna.

A ranar Lahadi aka yi jana’izar Folorunsho Ariyo bayan karbo gawarta daga inda ’yan sanda suka ajiye, Babban Asibitin Umaru Musa Yar’adua da ke Sabon-Wuse, Jihar Neja.

Wani shugaban yankin da aka tsinci gawarwakin, John Alpha Dogo, ya ce a daren Juma’a ne ’yan bindiga suka kai mutanen wurin suka yi musu kisan gilla.

Lamarin dai ya jefa mazauna yankunan Bagye da kuma Pashin da ke karkashin masarautar Dnata cikin tashin hankali inda suke ta kaura daga gidajensu. 

Aminiya ta gano cewa  a baya-bayan nan, ’yan bindiga sun addabi al’ummar masauta  Dnata, wadda aka ciro daga Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna a 2022.