Gawa ta mike bayan an binne ta da kwana bakwai

Mutanen wani kauye da ake kira Luk, wanda akasarinsu manoma ne da ke yankin Bunkupurugu-Yunyoo a Arewacin kasar Togo, sun shiga rudani bayan wata gawar matashi ta mike kwanaki bakwai kacal da binne ta. Saurayin mai suna Konkper-Laar Samuel, dan kimanin shekara 22, ya rasu ne bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya […]

Gawa ta mike bayan an binne ta da kwana bakwai

GE DIGITAL CAMERA

Mutanen wani kauye da ake kira Luk, wanda akasarinsu manoma ne da ke yankin Bunkupurugu-Yunyoo a Arewacin kasar Togo, sun shiga rudani bayan wata gawar matashi ta mike kwanaki bakwai kacal da binne ta.
Saurayin mai suna Konkper-Laar Samuel, dan kimanin shekara 22, ya rasu ne bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya inda aka binne shi a makabartar iyali da ke bayan gidansu.  Bayan an rufe shi ne tare da dora wa kabarinsa duwatsu da itatuwa tare da rubuta sunan mamacin a wani katako da aka soka a bisa kabarin mai dauke da suna da kuma ranar da ya rasu, sannan jama’a suka watse kowa ya kama gabansa kamar yadda al’adar garin ta bukata.
 Al’adar kauyen ta nuna, iyalan mamaci kan taru a gidansa ne a ranar da ya cika kwanaki bakwai da mutuwa, don tattauna batun gado da kuma basussukan da ake bin mamacin kafin a raba gado. Iyalan nasa sun taru ne da misalin karfe takwas na safe, amma kwatsam sai suka ga gawar ta koma gida sanye da tufafin da aka binne ta kwanaki bakwai da suka wuce.  Hakan ta sa wadanda suka taru don tattauna batun kowa ya ranta a cikin na-kare.  Wadansu daga ciki sun koma kabarin ne don tantance gaskiyar lamari, amma abin mamaki da isarsu sai suka tarar da kabarin yadda yake, watau babu alamar an bude shi ta kowace kusurwa, lamarin da ya kara tabbatar musu lallai fatalwar mamacin ce ta koma gida. Da labari ya sake bazuwa a kauyen ne, sai sauran mutane suka rika barin garin don fargabar abin da ka iya biyo baya.
Sai dai kafin nan, an samu labarin wani Limamin cocin yankin ya ziyarci gidan mamaci Samuel, inda ya yi masa wadansu tambayoyi da suka hada da na dalilinsa na tashi daga kabarinsa bayan an binne shi, inda mamacin ya bayyana cewa kakanninsa ne suka umarce shi da ya koma gida don lokacin mutuwarsa bai yi ba.
Rundunar ’yan sandan Togo ta yi wa garin tsinke inda ta kama “mamacin” kuma ta sanya masa ankwa kafin ta iza keyarsa zuwa ofishinsu don ci-gaba da bincike.