Gawa ta sanya mutane kuka da dariya a lokaci guda

Wani abin al’ajabi ya faru a unguwar ’Yar Gabas da ke cikin karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa a Jihar Sakkwato lokacin da wani mutum mai suna Alhaji Abdullahi Nuhu, mai shekara 62 ya dawo gida ya samu ’yan uwa da abokan arziki suna kokarin yi wa wata gawa sallah da ake zaton tasa ce.Malam Abdullahi, […]

Gawa ta sanya mutane kuka da dariya a lokaci guda

Wani abin al’ajabi ya faru a unguwar ’Yar Gabas da ke cikin karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa a Jihar Sakkwato lokacin da wani mutum mai suna Alhaji Abdullahi Nuhu, mai shekara 62 ya dawo gida ya samu ’yan uwa da abokan arziki suna kokarin yi wa wata gawa sallah da ake zaton tasa ce.
Malam Abdullahi, wanda yake sana’ar gini, Aminiya ta zanta da shi a gidansa da ke unguwar ’Yar Gabas domin sanin yadda wannan lamarin mai rikitarwa ya faru gare shi, inda ya bayyana cewa, “A ranar  Juma’ar da ta gabata ne na bar gidana da karfe dayan rana zuwa masallacin Shehu, bayan kammala sallah na wuce unguwar Gidan Igwai, domin a kullum nakan tafi can domin hutawa tare da abokan sana’ata. Na yi mamaki sosai da misalin karfe 6 na maraice (yamma) da na shigo unguwarmu, sai na ga yanayin fuskokin mutane gare ni ya canja, har wadansu samari suka yi shewa, amma ban damu ba, ina shiga kwanar gidana kawai sai na ga taron mutane a zazzaune cikin halin juyayi. Nan take suka zagaye ni, sai na tambaye su, me ke faruwa ne, sai suka gaya mini cewa, ‘Kai ne muke jiran a fito da kai mu yi maka sallah a kai makabarta, don an dade da gina rami (kabari) a makwancinka’. Sai na ce kamar yaya? Sai wani ya gaya mini cewa, ‘Wani jami’in asibitin kwararru ne da ke nan cikin gari ya zo mana da wani hoto yana tambayar ko an san mai wannan fuskar, sai iyalinka da ’yan uwanka gaba daya suka tabbatar kai ne ke cikin hoton, sai ya tabbatar mana da cewa ka rasu a sanadiyar bugewa da mashin (babur) ya yi maka, yanzu haka gawarka na dakin ajiye gawa na asibitin, yana tambaya ne har aka kawo shi nan. Ba da bata lokaci ba mutum bakwai suka tafi aka dauko gawar domin yi mata sutura, a halin da ake ciki yanzu mu a nan duk mun gama alwala muna jiran fitowa da kai ne domin a sallaci gawarka’.’’
“A lokacin da ya yi shiru, kaina ya kwance, sai na tambayi ina gawar take, aka ce tana ciki su liman ne ke shiryata. Da shigata na samu Liman Junaidu, sai ya yi mamakin ganina, nan take dai aka tabbatar ba ni ba ne. Na dubi fuskar mamacin sosai na ga lallai mun yi kama da shi, sai dai ni ina da wani tabo a fuskata, wanda shi ba ya da shi, amma kusan komai namu daya ne, kamanni ne ya sanya aka ce na mutu. A nan kuma sai juyayi ya koma farin ciki, duk wadanda suka yi kuka suka koma dariya. Babban dana ya je ya sanar da rundunar ’yan sanda ta Sakkwato ta Arewa, suka zo suka mayar da gawar asibiti. Tunda an gano ba ni ba ne ka ga ba maganar sallah, duk abokanaina na Gidan Igwai ba su samu labari ba, sai da lamarin ya wuce ya koma dariya, sa’annan hirar ta isa gare su”.
Da wakilinmu ya tambaye shi yadda ya ji lamarin, sai ya ce, “Wannan lamari ne daga Allah wanda Ya yi mana kamanni da wannan mutum kuma Ya kaddari sai an kawo shi gidana an yi masa wanka an sanya masa likkafani, inda Allah Ya taimake ni dai na dawo gida kafin a je a bizne wannan mutum, na gode wa Allah da Ya kawo lamarin cikin sauki da fahimta”.
Ya kara da cewa,  “Ina can Gidan Igwai a zaune dan uwana ya baro ni ya zo gida, don an kira shi a waya aka fada masa cewa  na rasu, shi kuma bai yi tunanin duba inda nake hira don sanar da abokaina abin da ke faruwa ba, don kawai Allah Ya kaddari sai an dauko wannan mutum daga asibiti”.
Liman Malam Junaidu, wanda shi ne limamin unguwar da  ya yi wa gawar wanka, a zantawarsa da Aminiya ya ce, “Gawar da aka kawo mana ta wannan mutum a wannan lokacin, gaskiya ban ga wani bambanci da ke tsakaninsu da wannan makwabcinmu dan uwanmu ba, a wannan lokacin ba wani mutum da zai ce maka suna da bambanci, a zahiri kamanninsu daya ta ko’ina. Bayan mun gama yi masa wanka, sai ga Abdullahi ya dawo. Mun dauki wannan lamarin kawai kowane bawa, idan Allah Ya yi nufin ya rufa masa asiri, Yakan rufa masa ta ko’ina, duk da an saya mana natsuwa ga wannan sifar ta wani a matsayin dan uwanmu, tunaninmu ya ba mu wannan lamari ne daga Allah da Ya tsayar da fahimtarmu ga wannan mutum har muka dauko shi muka yi masa sutura, abin da zai kara nuna maka wannan aikin Allah ne kawo hoton ma a wurinmu da jam’in asibiti ya yi”.
Abubakar Abdullahi, wanda shi ne babban dan Abdullahi ya ce, “Mu bakwai muka tafi asibiti, mun ga gawar lallai kamaninsu daya da mahaifinmu, shi ne ya sa muka dauko shi don yi masa sutura. Ba mu yi tunanin kiransa a waya ba, don ba shi da waya, ya daina sayenta ne don a koyaushe ya saya takan bace. Mun gama yi masa wanka, muna yin alwala kawai sai ga mahaifinmu ya dawo a kan babur na haya”.
Ita kuwa matar Malam Abdullahi cewa ta yi, a lokacin da aka zo da gawar ba ta je ta ganta ba, domin da ta je kila da hakan ba zai faru ba, don ta san kalar kayan da yake sanye da su a lokacin da zai je masallaci, “Kuma mun san yakan je Gidan Igwai a kullum”.