Gawa ta tashi bayan an yi jana’izarta da kwana 13
Gawar wata mata Sharolyn Jackson ta tashi, wadda ta bayyana bayan kwana 13 da jana’izarta, inda ’yan uwanta ke da tabbacin sun binneta, kamar yadda Gidan talabijin na CBS ya nuna hoton. Don haka mai sharhi, ya bijiro da tambaya kan cewa “Kusan kowace al’ada da addini suna da lokutan da suke kebancewa don karrama […]
Gawar wata mata Sharolyn Jackson ta tashi, wadda ta bayyana bayan kwana 13 da jana’izarta, inda ’yan uwanta ke da tabbacin sun binneta, kamar yadda Gidan talabijin na CBS ya nuna hoton. Don haka mai sharhi, ya bijiro da tambaya kan cewa “Kusan kowace al’ada da addini suna da lokutan da suke kebancewa don karrama mamaci, to ko akwai shirin da ake yin a tarbar wanda aka binne ya komo a raye?”
Zuri’ar Sharolyn Jackson sun gano ’yar uwarsu mai shekara 50 bayan kwana 13 da suka yi mata jana’iza.
A cewar mai gabatar da shirin talabijin na CBS, Philly KYW, wannan al’amari ya auku ne bayan da aka kai rahoton batan wannan mata daga gidansu da ke Yammacin Philadelphia. Sai hukuma ta samu gawar da ta yi kama da ita, kuma mutum biyu, har da danta na cikinta suka tabbatar Sharolyn Jackson ce.
Jackson ta “mutu” a ranar 20 ga Yulin bana, kuma an buga bayanan mutuwarta a jaridar The Time of Trenon, danginta sun binneta a ranar uku ga watabn Agustar bana, har wani ma ya rubuta a littafin ta’aziyyarta cewa kuyi hakuri, don “Ubangiji ke yin kiran karshe.”
A halin yanzu dai wadannan iyalai na aiki tare da hukumomi don ganin an tono wadda suka binne, ta yadda za a tantance ko ita wace ce.
A tsarin Sashen kula da lafiya na Philadelphia, matukar dangi suka tabbatar gawa ta su ce, ballantana na ciki, sai a tabbatar da gaskiyar hakan, a cewar Mai magana da yawun sashen, James Garrow, kamar yadda ya bayyana wa jaridar Huffington. Har yanzu ba a tantance lokacin da za a tonon gawar ba, ballanta a warware wannan matsala mai rikitarwa.
Aukuwar wannan lamari ba shi ne na farko ba, domin an taba binne wani mutumin Brazil Giberto Araujo, inda aka tabka kuskure a shekarar da ta gabata. (gawar da aka binne ta wani abokin aikinsa ce). Sai kawai daga bisani ga shi ya bayyana, inda ya samu ’yan uwa da abokan arziki na jimamin makokin mutuwarsa, sai kawai ya ce musu “kai ni fa ina nan a raye.”