Gawuna ya ɗauka zai ci banza kamar yadda Ganduje ya ci a 2019 — Kwankwaso
Ba a taba yin abun da aka yi addu’a a Kano da kasar nan da kasashen duniya kamar shari’ar Abba ba.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a Zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi tunanin zai ci banza wajen samun nasara a ɓagas.
Kwankwaso na wannan furuci ne a hirarsa da TRT Hausa jim kadan bayan Kotun Koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Kano.
- Bayan rahoton Aminiya gwamnati ta waiwayi gidan marayu na Kirista a Gombe
- Hukuncin Kotun Ƙoli kan zaben gwamnoni ya ɗaga martabar dimokuraɗiyya — Atiku
Sanata Kwankwaso ya fara jawabinsa ne da nasiha mai hade da gugar zana ga takwaransa kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, kan cewa nan gaba kadan zai fahimci ya yi asara saboda kura-kuran da ya tafka.
Ya ce, “shi [Ganduje] ne babban wanda ya tafka asara a shari’ar da Kotun Koli ta tabbatar wa Abba Kabir Yusuf mukaminsa na gwamnan Kano.
“Ba ni da wani labari ko wani sako. Ai mai girma tsohon shugaban kasa ya ce jiki magayi. Duk abin da za ka yi, ka zama mai daraja. Kada ka yarda ka zubar da mutuncinka kamar yadda suka zubar da mutunci,” in ji Kwankwaso.
“Ka ga mutunci madara ne idan ya riga ya zube shikenan ya lalace. Na tabbata shi [Ganduje] shi ya fi kowa asara domin ba zai gane asarar ba sai nan gaba kadan. Daga shi sai wanda ya yi takarar gwamna Gawuna,” in ji Kwankwaso.
“[Gawuna] Ya dauki layi na mutunci da daraja ya yarda bai ci zabe ba. Amma zama da madauka kanwa suka je suka zuga shi ya zo ya dauka cewa ga wata banza ta fadi kawai zai ci banza shi ma kamar yadda mai gidansa [Ganduje] ya ci banza a shekara ta 2019.
“Wannan duka darasi ne. Kowanne daga cikinsu da mu da muke wannan bangare na NNPP ko Kwankwasiyya da jama’ar Jihar Kano da Nijeriya har ma shi da kansa shugaban kasa da ya fi samun kwanciyar hankali da ba su kai karar nan ba.
“Amma mafi muhimmanci a wurinmu mu da ba sa sonmu yanzu sun yi wani abu da ya jawo wanda ake cewa tun da aka yi Jihar Kano a sanin masana da masu shekaru ba a taba yin abubuwa da aka yi addu’a a Kano da kasar nan da kasashen duniya kamar wannan ba,” inji Kwankwaso.
‘Inganta ilimi da tsaro muka sa a gaba yanzu’
A hirar tasa daii ta TRT Huasa, Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta NNPP halin yanzu za ta mayar da hankali domin yi wa al’ummar jihar Kano ayyuka.
“Mu dama a tsarinmu tsari ne na harkar ilimi. Harkar ilimin nan a nan aka sanmu da ita kuma ita ce karfinmu. Na tabbata ita ce ta fi dukkanin abubuwa da za ka iya tunani na harkar gwamnati,” in ji Kwankwaso.
“Amma yanzu da yake harkar tsaro ta shigo, ko yau din nan mun yi magana da mai girma gwamna ya gaya mini irin abubuwan da yake so ya yi na tsare-tsare wanda za a kawo a jihar Kano.
“Idan Allah ya yarda gwamnatin Kano za ta dauki mataki na kare al’ummarta a zauna lafiya a yi ilimi a yi noma a yi sana’o’i da sauransu domin kasa ko jiha ta ci gaba. Idan Allah ya yarda sai Kano ta zama jihar misali daga nan zuwa shekara hudun nan ko uku da suka rage na wannan mulki,” kamar yadda Sanata Kwankwaso ya kara da cewa.
Shawara ce tsakanina da Abba — Kwankwaso
Haka kuma, a wata hira mai nasaba da nasarar da NNPP ta samu da ya yi da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce shawara ce kawai tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayinsa na jagora.
A cikin hirar, Kwankwaso ya ce ko kaɗan ba shi da hurumi kuma ba zai iya juya akalar gwamantin Kano ba sabanin yadda wasu ke zargi.
“Ko ɗan da ka haifa ba za ka je ka zauna ƙofar ofishinsa ba ka ce kai za ka riƙa fada masa abin da zai yi ba, amma shawara tun kafin a kafa gwamnati nake cewa zan bayar da shawara, kuma ina bayarwa daidai gwargwado, kuma na tabbata akwai ire-irena da ke da niyar bayar da shawara.”
‘Babu wata yarjejeniya tsakaninmu da Tinubu’
Kwankwaso ya kuma ce sabanin zargin da wasu ke yi, babu wata yarjejeniya da ya kulla da Shugaban Kasa Bola Tinubu ko kuma wani dangane da sakamakon hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan shari’ar zaben gwamnan Jihar Kano.
“Abin da na sani shi ne lokaci daya na yi suna a fannin siyasa tare da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu. Na shiga siyasa lokaci daya tare da shi a SDP. Sannan ya zama Sanata, ni kuma na zama Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai. A shekarar 1999 muka zama takwarorin juna, ya zama Gwamnan Jihar Legas ni kuma na zama Gwamnan Jihar Kano.
“Tare muka kafa APC kuma mun taka rawa sosai a duk fafutukar da ta biyo baya. Ya kamata mutane su sani cewa karya gajeran zango take ci. Duk da makircin da mutanen suka yi, alkalai sun yi abin da ya dace.
“Saboda haka babu wata matsala. Suna da jam’iyyarsu; muna da tamu. Za mu yi aiki tare idan bukatar hakan ta taso da kuma wuraren da suka cancanta. Dangane da batun shiga ta gwamnati lokaci ne kawai zai fayyace hakan.”