Gawuna ya taya Abba Gida-Gida murnar lashe zaben Gwamnan Kano
Matakin na zuwa ne mako daya da bayyana sakamakon
Bayan mako daya da bayyana sakamako, dan takarar Gwamnan Jihar Kano a jamiyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya mika sakon taya murna ga zababben Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.
Gawuna wanda kuma shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar ya mika wannan sakon ne a cikun wani faifan murya da Mataimakinsa kan harkokin Watsa Labarai, Hassan Musa Fagge ya fitar ya aike wa Aminiya.
Sakon na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba Abba na jam’iyyar NNPP shaidar lashe zaben a Kano.
Gawuna ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne duba da cewa duk da korafin da suka yi wa Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Kasa kan ta sake bibiyar zaben amma a maimakon hakan sai ta bayar da shaidar cin zabe ga dan takarar Jamiyyar NNPP.
“Kowa na sane da cewa mun rubuta wa Hukumar INEC korafinmu akan zaben da aka gudanar ranar Asabar 18 ga Maris, wanda muka nemi ta sake gudanar da zabe a wasu wutare da wadancan abubuwa suka abku sabanin sanarwar da ta bayar cewa dan takarar Jamiyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben, amma sai ga shi a yau 29! ga watan Maris Hukumar INEC ta kara tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ta hanyar ba shi takardar shaidar lashe zabe”
Gawuna ya yi kira ga magoya bayansa da su karbi kaddara.
“Dama tun a baya mun sha fadi cewa idan lamarin nan alheri ne Allah Ya ba mu idan kuma ba alheri ba ne to muna rokon Allah Ya canza mana da mafi alheri. Don haka nake kira ga magoya baya da su zama masu karbar kaddara”
Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida fatan alheri tare da yin adduar Allah Ya sa ya zama shugaba mai adalci.
“Muna yi wa wanda Allah Ya ba wa adduar Allah Ya sa ya zama shugaba nagari mai yin adalci ga kowa. Allah Ya sa mu kuma mu zama masu biyayya ga shugabanci”