Gawuna ya wakilci gwamnatin Kano wurin yi wa Kwankwaso ta’aziyya

Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar zuwa gidan tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso don ta’aziyyar

Gawuna ya wakilci gwamnatin Kano wurin yi wa Kwankwaso ta’aziyya
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar zuwa gidan tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso don ta’aziyyar rashin mahaifin sa.
Da sanyin safiyar Juma’a ne dai Allah ya karbi ran mahaifin tsohon gwamnan, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso wanda shine Hakimin Madobi kuma Makaman Karaye yana da shekaru 93 a duniya.

Tawagar gwamnatin da ta kunshi Kwamishinoni da ma su ba gwamnatin shawara da shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar.

Yayin jawabinsa na ta’aziyyar, Mataimakin gwamna Nasiru Gawuna ya ce, “A madadin gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, muna mika sakon ta’aziyyar mu gare ka bisa rashin mahaifinmu marigayi Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, Makaman Karaye.

“Hakika, rashin sa babban rashi ne da ba kai kadai ya shafa ba, rashi ne da ya shafi mutanen Kano baki daya”.

“Muna Addu’ar Allah yasa shi a Jannatul Firdaus, ya kuma bayar da hakurin rashin dattijon arziki da aka yi,” In ji Gawuna.

A nasa jawabin tsohon gwamna Kwankwaso, ya godewa mataimakin gwamnan sakamakon ziyarar da ya kai masa ta ta’aziyyar.

A wani labarin kuma, Mataimakin Gwamnan har ila yau ya jagoranci tawagar zuwa Gidan Kadiriyya don yi musu ta’aziyyar rasuwar ‘yar uwa su, Hajiya Maryam Nasiru Kabara.

Gawuna ya yi addu’ar Allah jikan ta ya kuma ba su hakurin jure babban rashin.

Rahotanni dai sun nuna cewa tun ranar Alhamis da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bar Kano zuwa Dubai, ana jajiberin mahaifin Kwankwason zai rasu kenan.