Gayyatar Rahama Sadau muka yi —’Yan sanda
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta gayyaci Rahama Sadau zuwa ofishinta ne amma ba tsare jarumar ta yi ba kamar yadda ake rade-radi. Majiyar ’yan sanda a jihar ta shaida wa Aminiya cewa Shugaban ’Yan Sandan NajerriyaMohammed Adamu ne ya umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya gudanar da […]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta gayyaci Rahama Sadau zuwa ofishinta ne amma ba tsare jarumar ta yi ba kamar yadda ake rade-radi.
Majiyar ’yan sanda a jihar ta shaida wa Aminiya cewa Shugaban ’Yan Sandan NajerriyaMohammed Adamu ne ya umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya gudanar da bincike kan rudanin da hotunan da jarumar ta masana’antar fina-finai ta Kannywood ta wallafa, wanda ya kai ga wani mutum daga cikin masu sharhi a kan hotunan ya yi batanci ga Manzon Allah S.A.W.
- ‘Yan Kannywood sun yi tir da hotunan Rahama Sadau
- Rahama Sadau ta yi nadamar batancin da hotunanta suka jawo
- Kungiyar shirya fina-finai ta dakatar da Rahama Sadau
- Ya kamata a tausaya min saboda halin da na shiga —Rahama Sadau
Majiyar ta kara da cewa Rahama Sadau ta koma Abuja tare don gudun kada a farmake ta a Kaduna, kafin daga bisani hukumar ’yan sandan ta gayyace ta zuwa Kaduna domin amsa tambayoyi.
Gayyatar na zuwa ne bayan wani mai suna Mallam Lawal Mohammed Gusau ya shigar da korafi a kan jarumar a ranar 3 ga watan Oktoba 2020, dangane da batancin da hotunan da ta wallafa suka jawo wa Manzon Allah (SAW).
Kafin shigar da kara a kanta, Rahama Sadau ta bayyana a wani bidiyo a yanayi na ban tausayi da nadama, inda ta nemi afuwar dukkanin Musulmi game da lamarin.
Har wa yau, a yayin hirarta da sashen Hausa na BBC, jarumar ta bayyana cewa ya kamata jama’a su tausaya mata domin ta fi kowa shiga damuwa a kan lamarin.