Gaza: Al’ummar Duniya Na Zanga-zangar Ƙin Jinin Isra’ila
An gudanar da zanga-zangar adawa da Isra’ila a Gabas ta Tsakiya ta Turai da Amurka da Indiya da Pakistan da kuma Gabashin Asiya
Dubban mutane a fadin duniya sun gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen yakin da da Isra’ila ta ƙaddamar a Zirin Gaza da kuma Lebanon.
Masu zanga-zangar sun la’anci hare-haren na Isra’ila, inda suka bayyana abin da ke faruwa a Gaza a matsayin kisan kiyashi, suna masu kira ga hukumomini duniya su taka mata burki.
An gudanar da irin wannan zanga-zanga a fadin yankin Gabas ta Tsakiya ta Turai da Amurka da Indiya da Pakistan da kuma Gabashin Asiya.
Isra’ila ta kashe Palasdinawa sama da 41,615 a Zirin Gaza tun daga lokacin da ta kaddamar da kazamin hari a yankin a watan Oktoban 2023.
Hare-haren da tankoki da jiragen Isra’ila suka kai ta kasa da sama da kuma ruwa sun raba sama da Palasdinawa miliya 2.5 da muhallansu.
Sun kuma rusa ababen more rayuwa da asibitoci da wuraren ibada da makarantu da sansanonin ‘yan gudun hjira a Gaza.