Gaza: Amurka ta nemi a fadada yarjejeniyar tsagaita wuta

Sakataren Harkokin Wajen kasar Amurka, John Kerry ya nemi Isra’ila da Falasdinawa da su yi amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma  ranar Talata wajen fadada tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu a fatan ganin dorewar zaman lafiya a yankin.A wata zantawa da ya yi da BBC shekaranjiya  Laraba, Mista Kerry, ya ce akwai bukatar […]

Gaza: Amurka ta nemi a fadada yarjejeniyar tsagaita wuta
Gaza: Amurka ta nemi a fadada yarjejeniyar tsagaita wuta

Sakataren Harkokin Wajen kasar Amurka, John Kerry ya nemi Isra’ila da Falasdinawa da su yi amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma  ranar Talata wajen fadada tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu a fatan ganin dorewar zaman lafiya a yankin.
A wata zantawa da ya yi da BBC shekaranjiya  Laraba, Mista Kerry, ya ce akwai bukatar bangarorin biyu su mayar da hankalinsu wajen tabbatar da kafuwar kasashe biyu.
Kerry ya ci gaba  da cewa Isra’ila na da ‘yancin kare kanta daga hare-haren rokoki da Falasdinawa ke kai mata, sannan kuma ya dora laifin farmakin a kan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. Majalisar dinkin Duniya ta yi marhabin da matsayar da aka cimma, tare da fatan cewa bangarorin biyu za su mutunta ta.
Dangantaka tsakanin Isra’ila da Falasdina ta yi tsami ne bayan kisan wani saurayi Bafalasdine, Muhammad Abu Khdeir a farkon watan jiya. Wanda kuma hakan ya janyo mummunar tarzomar daga bangaren Falasdinawan, bayan da aka fara yada rade radin cewa kisan ramuwar gayya ce da wasu Yahudawa masu tsatsauran ra’ayi suka aikata kan kisan wasu matasan Yahudawa uku a cikin watan Yuni.