Gaza: An gano gawarwaki 49 a Asibitin Al-Shifa
Lamarin na da matuƙar ban tsoro yayin da Isra’ila ke tsananta kai hare-hare a faɗin yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa akasarin gawarwakin Falasɗinawa 49 da aka gano a cikin Asibitin Al-Shifa sun ruɓe.
Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza ne ya tabbatar da cewa sun gano gawarwakin waɗanda cikinsu wasu babu kai.
- ’Yan bindiga sun kashe ma’aikatan kamfanin manja 3 a Edo
- Ya Kashe Matarsa Kan Zuwa Ganin Danta A Gidan Tsohon Mijinta
Motassem Salah, shugaban sashen bayar da agajin gaggawa na Asibitin Al-Shifa, ya shaida wa manema labarai cewa “an gano babban kabari na uku a cikin wannan asibiti.
“Wannan yana da matuƙar ban tsoro kuma yana ba jefa fargaba game da abin da ke faruwa a cikin unguwannin a lokacin harin Isra’ila.”
Ya zuwa yanzu jimillar gawarwakin da aka gano sun kai 520 a Asibitin Al-Shifa, Asibitin Nasser da ke Kudu tare da Asibitin Kamal Adwan da ke Arewacin yankin.
A watan da ya gabata, an gano gawarwaki kusan 30 da aka binne a wasu kaburbura biyu a harabar Asibitin na Al-Shifa.
Wannan lamari dai na da matuƙar ban tsoro yayin da Isra’ila ke tsananta kai hare-hare a faɗin yankin cikin sa’o’i 24 da suka gabata.