Gaza: Iran ta yi barazanar shiga yakin Isra’ila da Hamas

Gargadin na zuwa ne yayin da yawan wadanda Isra’ila ta kashe a Gaza ya haura 11,000

Gaza: Iran ta yi barazanar shiga yakin Isra’ila da Hamas

Kasar Iran ta yi barazanar shiga yakin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa muddin Isra’ilar ta ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Hossein Amirabdollahian ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da takwaransa na Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, kamar yadda gidan talabijin din Iran na Press TV ya rawaito ranar Juma’a.

Hossein ya kuma ce, “Saboda yadda Isra’ila ta zafafa kai hare-hare a kan fararen hula a Gaza, babu makawa sai mun shiga yakin nan.”

Sai dai ba a san hakikanin abin da yake nufi da “shiga yakin” ba.

Kazalika, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, Ministan ya ce, “Lokaci na dada kurewa da za mu zauna mu zuba ido Isra’ila na ci gaba da tabargaza.

“Amfanin Netanyahu guda daya shi ne ya aza harsashin rushewar gwamnatin Isra’ila kuma hakan ya nuna irin zalinci da danniya da Yahudawa ke ci gaba da yi na yin kisan gilla ga mata da kananan yara a Gaza.

“Babu makawa makoma a nan gaba ta Falasdinawa ce,” in ji Ministan.

Ana dai ci gaba da zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da harin rokoki a kan Isra’ila, ita kuka tun lokacin ta ci gaba da mayar da martani ta hanyar yin luguden wuta a kan Falasdinawa.

Ya zuwa yanzu dai, bayanai na nuni da cewa yawan mutanen da Isra’ila ta kashe sun hara 11,000.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa