Gaza: Islamic Jihad ta kai wa sojojin Isra’ila hari a Khan Younis
Mayaƙan kungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad da ke Gaza, sun kai wa sojojin Isra’ila hari a yankin Khan Younis
Rundunar Al-Quds Brigades, ta kungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad da ke Gaza, ta ce mayakanta sun kai wa sojojin Isra’ila “hari a yankin Khan Younis”.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Telegram, ta ce an kai wa sojojin hari da “bama-bamai”, ba tare da karin bayani kan harin ba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin harin da Isra’ila ta kai ta sama ya hallaka Falasɗinawa kusan 30 tare da jikkata wasu da dama a birnin Deir el-Balah.
Yanzu yankin na Deir el-Balah, wanda aka ware a matsayin mai tsaro a makonnin farko na yakin, ya zama wurin da ake kai hare-hare ta sama.
- Gobara ta kone shaguna 20 a kasuwar Ibadan
- Yadda Talakawa Za Su Biya Karin Dalar Da Akan Yi Wa Masu Shigo Da Kaya Ta Kago
A nan ne kuma dubban mutanen da aka ba da umarnin ficewa daga arewacin birnin Gaza suke zama.
A ’yan kwanakin nan Isra’ila ta tsananta kai hare-hare ta sama a yankin tsakiyar Gaza, inda sojojinta suka janye a ‘yan kwanakin baya.
Tun da sojojin Isra’ila suka janye ta addabi yankin da hare-haren wuce gona da iri da kuma harba makaman roka.
Hare-haren da aka kai a yammacin birnin, sun gagarumar barna ga gidaje da sauran matsugunan jama’a.
Hakan ya sa ba za a iya kuka da yawancin mutanen da suka samu raunuka ba nan take a asibiti, kuma suna iya mutuwa a inda suke kwakkwance a kasa a asibitin.