Gaza: Isra’ila ta kashe mutum 195 a sansanin gudun hijira
Kungiyar Hamas ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe mutum 195 a sansani Gudun Hijira na Jabaliya da ke Zirin Gaza a cikin kwana biyu

Gawar wata Bafalasdiniya, Ayham Sahfei, da Isra’ila ta kashe a yankin Ramallah da ke Gabar Yammacin Kogin Jordar a ranar Alhamsi 2, ga Nuwamba, 2023. (Hoto: Zain Jaafar/AFP)
Kungiyar Hamas da ke iko da Zirin Gaza ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe mutum 195 a sansani Gudun Hijira na Jabaliya a cikin kwana biyu.
Hamas ta sanar cewa, “wadanda hare-hare biyu da Isra’ila ta kai a sansanin Jabalia ya haura 1,000 ciki har da wadanda da suka rasu da wadanda suka jikkata.”
- Saudiyya ta kaddamar da gidauniyar tallafa wa Falasdinawa
- ’Yan bindiga sun kashe matafiya sun sace wasu a Zamfara
Sanawar da kungiyar ta fitar ta ce, hare-ahren na ranakun Talata da Laraba sun “yi ajalin mutum 195, wasu 120 sun bace, baya ga wasu 777 da aka jikkata.”