Gaza: Isra’ila ta kashe Palasdinawa 23,968 ta jikkata 60,582 a kwana 100
Sai kananan yara sun yi roko kafin su samu ruwan sha a Gaza
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa kimanin 23,968, suka kuma jikkata wasu 60,582 a cikin kwana 100 da suka gabata a Zirin Gaza.
Akasarin wadanda wannan aika-aika ta fi shafa kananan yara da mata da tsofaffi ne a Gaza, inda a halin yanzu Falasdinawa sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu, sannan sai kananan yara sun roka kafin su samu ruwan da za su sha.
Babban Jami’in Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Philippe Lazzarini, ya ce, hakan na faruwa ne “duk da gargadin da muka yi kan wannan bala’i,” a Gaza inda kishirwa da yunwa da damuwa suka addabi Falasdinawa.
“Duk lokacin da kuka je makaranta, yaran suna kallon ku suna rokon ku ruwan da za su sha ko burodin da za su ci,” in ji shi, da yake siffanta halin da yaran Falasdinawa ke ciki a matsuguni da makarantu da Hukumarsa ke gudanarwa.
- NAJERIYA A YAU: Mece Ce Makomar Jam’iyyar APC A Jihar Kano?
- Pantami ya samo N50m daga kudin fansan ’yan uwan Nabeeha
A wata sanarwa, gwamnatin Falasdinu ta ce, duk barnar da Isra’ila ke yi a Falasdinu, “kasashen duniya sun kasa aiwatar da kudurorin kasa da kasa da suka shafi lamarin.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen ta ce Falasdinu A kwanaki 100 da suka shude “Isra’ila ta mamaye Gaza ta kuma mayar da yankin kufai, ta hanyar kisan gilla da kuma tilasta wa mutane kusan miliyan biyu gudun hijira.
“Kwanaki 100 sun shude Isra’ila da wa Falasdinawa na wannan kisan gilla, amma abin al’ajabi har yanzu wasu kasashe sun makance, ba su gamsu cewa kisan gilla ya isa zama dalili su daina goyon bayan wannan aika-aika da Isra’ila ke yi ba.
Lallai ya kama kamata wadannan kasashe su sauya tunani kan irin goyon bayan da suke baiwa Isra’ila,” in ji ma’aikatar.
A halin da ake ciki kuma, hare-haren da Isra’ila ta kai cikin dare ta sama da ta kasa a Gaza sun kashe Falasdinawa fiye da 100 tare da jikkata wasu da dama, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu, Wafa, a ranar Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran ya ce, an ciro gawarwakin fararen hula 50 daga baraguzan gini bayan harin bam din Isra’ila a wani bene mai hawa uku a unguwar Al-Daraj a tsakiyar birnin Gaza.
Yawancin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata an kai su zuwa asibitin Al-Shifa da kuma asibitin Baptist Baptist da ke birnin.
A wani harin na daban kuma, Falasdinawa 5 ne suka mutu, wasu 10 suka samu raunuka sakamakon harbin da sojojin Isra’ila suka kai a yankunan Sabra da Al-Zeitoun da ke birnin.
Har ila yau sojojin na Isra’ila sun kai hare-hare kan gidajen Falasdinawa da ke zaune a yankunan Tal Al-Hawa da Sheikh Ajleen da ke Kudu maso yammacin birnin Gaza.
A Khan Younis, an kashe Falasdinawa sama da 30 da suka hada da yara da mata a wani harin bam da Isra’ila ta kai kan gidajensu.
Akalla mutane 23 ne suka mutu a hare-haren da aka kai ta sama a wasu gidaje biyu da ke kusa da iyakar Masar da kuma kan wata mota mai dauke da fasinjoji, mafi yawansu da suka rasa matsugunansu.