Gaza: Kasashen Latin Amurka sun fara daukar mataki kan Isra’ila
Ba Bolivia ce kasar Latin Amurka da ta fara daukar matakan diflomasiyya a kan Isra’ila ba.
Kasashen Latin Amurka da dama sun fara daukar matakin yanke huldar diflomasiyya tsakaninsu da Isra’ila, kan abin da suka kira laifukan yakin da take aikatawa a Gaza.
Bolivia ce ta farko a kasashen Latin Amurka da ta yanke huldar diflomasiyya da Isra’ila a kan abin da ta bayyana da “takalar fada da amfani da matakin soja na fin karfi” a Gaza.
- Majalisa ta tabbatar da Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya
- ’Yan sanda sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa
Kasar ta yi kiran a tsagaita wuta kuma ta ce za ta aika kayan agaji zuwa Zirin Gaza da aka yi wa kofar rago.
Sai dai wani jami’in Isra’ila ya ce matakin tamkar “ba da hadin kai ne ga ta’addanci.”
Lior Haiat ya soki lamirin gwamnatin Bolivia da “alakanta kanta da kungiyar Hamas ta ’yan ta’adda.”
Mataimakin Ministan harkokin wajen Bolivia Freddy Mamani ya ce gwamnati ta yanke shawarar katse alakar ne “don nuna kin amincewa da kuma yin alla-wadai da matakin amfani da karfin soja na fin karfi da takalar fada a Zirin Gaza.”
Ya kara da cewa kasarsu na son kawo karshen kofar ragon da Isra’ila ta yi wa Gaza da hana “shigar da abinci da ruwa da kuma sauran muhimman kayan bukatun rayuwa.”
Sojojin Isra’ila sun yi wa Gaza tsinke tsawon makonni, inda muhimman kayan agaji ke shiga Zirin jefi-jefi ta hanyar iyakar Rafah daga kasar Masar kawai.
“Isra’ila ta yi alla-wadai da goyon bayan ta’addancin da Bolivia ta yi da kuma karbar gwamnatin kasar Iran, abin da ke nuni da akidojin gwamnatin Bolivia,” a martanin Mista Haiat.
Ana zargin Iran da bai wa Hamas goyon baya wajen kai hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba.
Sai dai yayin da shugabannin Iran suka nuna murna tare da yabawa ’yan bindigan da suka haddasa tarzomar, amma dai sun musanta hannu a lamarin.
Ba Bolivia ce kasar Latin Amurka da ta fara daukar matakan diflomasiyya a kan Isra’ila ba.
Shugaban Chile, Gabriel Boric a ranar Talata ya yi wa jakadan kasarsa da ke birnin Tel Aviv kiranye don gudanar da tuntuba “bisa la’akari da keta dokokin jin kai na duniya, wanda ba za a yarda da shi ba, da Isra’ila ke aikatawa a Zirin Gaza.”
“Chile cikin kakkausar murya tana alla-wadai kuma ta nunar da gagarumar damuwa cewa wadannan matakan amfani da karfin soja – wanda a wannan mataki ya kunshi ladabtar da daukacin al’ummar Falasdinawa fararen hula a Gaza,” kamar yadda ya rubuta a shafin X, wanda a baya ake kira Twitter.
Shugaban Colombia ma Gustavo Petro ya ba da irin wannan sanarwa a shafin sada zumunta.
Isra’ila dai na ci gaba da kai farmaki ta sama da kasa a yankin Zirin Gaza, tare da kaddamar da samame a wurare da dama a gabar Yamma da kogin Jordan, inda jami’na tsaronta suka kame Falasdinawa da dama.
A halin da aka ciki, kamfanin sadarwa na yankin Falasdinu ya ce an katse intanet da layukan wayoyi a yankin na Gaza baki daya, matakin da wata kungiyar agaji ta bayyana a matsayin kokarin yin rufa-rufa kan laifukan yakin da Isra’ila ke aikatawa.
Ma’aikatar kiwon lafiyar yankin na Falasdinu kuwa, gargadi ta yi ga kasashe game da halin da asibitoci ke ciki na rashin makamashi, tana mai cewa nan da wani lokaci man fetur din da suke da shi zai kare, matakin da ke tattare da gagarumar barazana ga Faladinawa da suka jikkata, wanda adadinsu ya zarta dubu 20 a halin yanzu, sai kuma fargabar rasa jarirai bakwaini da ake lura da lafiyarsu cikin na’ura.