Gaza: Kungiyar kasashen Musulmi ta kira taron gaggawa

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) ta kira taron gaggawa bayan Isra’ila ta shafe sama da wata guda tana luguden wuta a Zirin Gaza

Gaza: Kungiyar kasashen Musulmi ta kira taron gaggawa

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta Duniya (OIC) ta kira taron gaggawa kan yakin da Isra’ila ta shafe sama da wata guda tana yi a yankin Falasdinawa na Zirin Gaza.

Sanarwar taron na OIC na zuwa ne bayan Isra’ila da ke cin karenta babu babbaka a Gaza ta ba wa Falasdinawa wa’adin awa hudu su fice daga yankin Arewacin Gaza, lamarin da ya kara ja mata tofin Allah-tsine.

Taron wanda za gudana ranar Asabar a birnin Riyadh na kasar Saudiyya zai tattauna ne a kan yakin, wanda shi ne mafi muni da Isra’ila ta kaddamar a Gaza, inda ta kashe Falasdinawa sama da 10,000 wadanda akalla 4,000 daga cikinsu kananan yara ne.

Ta kuma raba miliyoyin Falasdinawa da gidajensu a Gaza, inda ta yanke ruwan sha da lantarki da man fetur, wanda hakan ke barazana ga rayukan daukacin Falasdinawa, musamman ma marasa lafiya da asibitoci suka daina aiki a sakamakon hakan.

A halin Isra’ila ta raba Gaza Gida biyu, inda sojojinta ke cin karensu babu babbaka, tare da neman kwace gudanar da tsaro bayan sun gama kwace yankin.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na fafutukar ganin an fitar da mutanen da rashin lafiyarsu ta tsananta matuka zuwa wasu kasashen ketare daga Gaza domin ci gaba jinya.

Kasashen Masar da Turkiya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun amince su karbi wasu daga cikin majinyatan.

Gabanin barkewar yakin na Gaza, Falasdinawa kimanin 20,000 a duk shekara suke neman izini daga Isra’ila don fita duba lafiyarsu, ciki har da kananan yara.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane 350,000 ne a Gaza suke fama da miyagun cututtuka irin su ciwon siga da kansa, baya ga mata 50,000 masu juna biyu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Jami’an lafiya sun yi gargadin cewa mutane da yawa na fuskantar barazanar rasa rayukansu a Gaza saboda rashin kula da lafiyarsu.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda