Gaza: MDD ta amince a tsagaita wuta nan take
Kashe 153 sun goyi bayan umarnin Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta nan take a Zirin Gaza
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ƙudurin tsagaita wuta nan take a yakin Falasɗinawa Zirin Gaza, inda Isra’ila ta kashe Falasɗinawa kimanin 20,000 tare da raba miliyoyi da gidajensu.
Kasashe 153 ne a suka kada kuri’ar amincewa da kudirin tsagaita wuta nan take da kuma ba da damar gudanar da ayyukan jin ƙai a Zirin Gaza.
Sai dai kashe 10 sun ki amincewa da kudirin a zaman Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniyar, ciki har da Amurka, Austria, Isra’ila, Jamhuriyar Czech da Paraguay da kuma kasar Liberia daga nahiyar Afirka.
Wasu 23 kuma suka kunne da kuri’a.
- Kisan Mauludi: Iyalan mutanen da aka kashe na neman diyyar N33bn daga Gwamnati
- Hayaniya ta kaure a Majalisar Kano kan kudaden masarautu
Majalisar Dinkin Duniya ta aiwatar da kudirin bayan a kwanakin baya Amurka ta hau kujerar na-ki kan tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke yi a yankin Falasɗinawa na Zirin Gaza.
Isra’ila ta kashe kimanin Falasɗinawa 20,000 bayan ga wasu Dubai da ta jikkata, waɗanda akasarinsu kananan yara da mata da kuma tsofaffi ne.
Duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya ke ta yi na dakatar da kisan kiyashin, Isra’ila ta ci ga da yin luguden bama-bamai ta kasa da sama a kan Falasɗinawa.
A halin yanzu Falasɗinawa kimanin miliyan daya da rabi daga cikin su kimanin miliyan biyu ne Isra’ila ta rusa gidajensu a Gaza.
A lokuta da dama sojojin Isra’ila kan kai hari da gangan su kashe daruruwan mutane a wuraren da suka umarci Falasɗinawa su je su fake.