Gaza: Sojan Amurka ya kona kansa a ofishin jakadancin Isra’ila

Wani sojan saman Amurka ya babbake kansa a ofishin jakadancin Isra’ila da ke kasarsa domin na nuna adawa da yakin Gaza.

Gaza: Sojan Amurka ya kona kansa a ofishin jakadancin Isra’ila

Wuta

Wani sojan saman Amurka ya cinna wa kansa wuta a wajen ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Washington DC, a wani mataki na nuna adawa da yakin Gaza.

Kafin cinna wa kansa wuta, sojan ya ce “ba ya goyon bayan kisan kiyashi” da Isra’ila ake yi  wa Falasdinawa a Gaza.

Bayan da ya cinna wa kansa wuta, ya yi ta ihun “Palestine ‘yanci” akai-akai.

Karo na biyu ke nan da Amurkawa ke cinna wa kansu wuta a wajen wata cibiyar Isra’ila da ke kasarsu, tun farkon yakin Isra’ila da Hamas.

Kafin wannan na ranar Lahadin, wani mai zanga-zanga ya cinna wa kansa wuta a wajen karamin ofishin jakadancin Isra’ila da ke Atlanta a watan Disambar bara, inda daga bisani aka gano tutar Falasdinawa a wurin.

Kimanin mutane 30,000 aka kashe a watanni hudu da yakin Isra’ila a Gaza bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga Oktoba, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.  

Kasa da mako guda ke nan bayan Amurka ta yi fatali da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na neman a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza.

Ko da yake ana ci gaba da tattaunawa kan tsagaita wuta na wucin gadi don saukaka sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yana ci gaba da  kare matakin sojin da kasarsa ta dauka a Gaza.