Gaza: Sudais ya yi tir da harin Isra’ila kan Falasɗinawa

Sudais ya ce Saudiyya na goyon bayan gwagwarmayar Falasɗinawa na kwato Masallacin Kudus daga hannun Yahudawa da kuma ganin Birnin Kudus ya zama babban birnin kasar Falasɗinu mai cikakken ’yanci

Gaza: Sudais ya yi tir da harin Isra’ila kan Falasɗinawa

Gawarwakin yaran wani Bafalasdine Abu Quta a harin da sojojin Isra’ila suka kai garin Rafah da ke Kudancin Zirin Gaza, a yayin janai’zarsu ranar 8 ga Oktoba, 2023 bayan kasamin fada tsakanin Hamas da Isra’ila. (Hoto: SAID KHATIB / AFP)

Shugaban Majalisar Masallatan Harami, Sheikh Abdul Rahman Sudais, ya bayyana goyon bayansa ga Falasɗinawa tare da yin Allah-wadai da hare-haren Isara’ila a Zirin Gaza.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Sudais ya ce ƙasar Saudiyya za ta ci gaba da goyon bayan Falasɗinawa a matsayin ’yan uwanta, domin ganin sun samu ’yanci a kasarsu, sun rayu cikin martaba, su cim-ma burinsu.

Sudais ya kara da cewa Saudiyya na goyon bayan gwagwarmayar Falasɗinawa na kwato Masallacin Kudus daga Yahudawan Isra’ila ’yan share-wuri-zauna, da kuma ganin Birnin Kudus ya zama babban birnin kasar Falasɗinu mai cikakken ’yanci.

Ya kuma la’anci hare-haren Isra’ila kan Masallacin Kudus da sauran wurare masu alfarma a yankin Gaza da sauran sassan Falasɗinu.

“[Yahudawa] Sun keta hurumin wurare masu alfarma tare da tauye haƙƙi da ’yancin Falasɗinawa da ba su ji ba, ba su gani ba,” in ji Sheikh Sudais.

Ya bayyana cewa a yayin da Saudiyya ta jajirce don ganin an samu wanzajjen zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, haƙƙi ne na addini da kuma ’yan uwantaka a kanta na ta kare Masallacin Kudus da kuma goyon bayan ’yancin Falasɗinawa da kasarsu da kuma martabarsu.

Don haka za ta ci gaba da goyon bayan Falasɗinawa har sai sun samu ’yanci, sun ƙwato ƙasarsu da aka mamaye, a kuma samu zaman lafiya a yankin.

Haka zalika za ta ci gaba da goyon bayan duk abin da ya shafi cigaban Musulmi da Musulunci a ko’ina a fadin duniya.