Gazawar gwamnati ya kawo rashin tsaro a kasa – Sultan
Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa gazawar Gwamnati ce ta kawo rashin tsaro a kasar nan. Domin kuwa a cewarsa idan gwamnati ta mike tsaye ta hanyar zartar da abinda ya da ce za ta magance matsalar. Sultan ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wajen taron majalisar Sarakunan Arewacin kasar nan […]

Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa gazawar Gwamnati ce ta kawo rashin tsaro a kasar nan. Domin kuwa a cewarsa idan gwamnati ta mike tsaye ta hanyar zartar da abinda ya da ce za ta magance matsalar. Sultan ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wajen taron majalisar Sarakunan Arewacin kasar nan da aka yi a Kaduna ranar Litinin da ta wuce.
Ya ce a matsayinsa na shugaban fulanin kasar nan da kuma yankin Afirka maso Yamma ba zai taba yarda ya umurci wani bafulatani ya dauki makami ya kashe wani mutum ba. Dan haka sai Sultan din ya ce masu kashe mutane da sunan fulani ‘yan ta’adda ne, kuma ana iya samun su a kowace kabila.
“idan ka ga abubuwa irin wannan na faruwa akwai gazawar gwamnati wajen ayyuwatar da ayyukanta, domin idan gwamnati na yin abin da ya dace hakan ba zai faru ba. Mun dade muna kira ga jama’a da su zauna lafiya. Su bar hukuma ta dauki mataki mu kuma zamu cigaba da matsawa hukuma har sai sun dauki matakan da za su kawo maslaha ga irin wadannan matsaloli.
“A matsayina na shugaban Fulani ba zan taba yin kira ga fulani ya dauki makami ya kaiwa wani hari da nufin kashe shi ba. Na zauna da mutane masu yawa na kuma san matsalolinsu, dan haka ba zan taba yarda bafulatani ya dauki makami ya kashe wani ba. Na jima ina cewa a wuraren taruka irin wannan cewa duk masu daukar makami suna kashe mutane ‘yan ta’adda ne. Ko inyamuri ne ko Bayarbe ko kuma Bahaushe. Ko fulani baka da yancin kashe wani mutum,” in ji shi.
Sultan ya kuma bayyana cewa halartar sarakunan kudancin kasar nan wajen taro alama ce dake nuna kasancewar su ‘yan kasa daya al’umma daya. “’yan uwanmu daga kudu sun halarci taron nan ne domin mun yarda mu zauna tare a matsayin ‘yan kasa daya kuma al’umma daya. Burin mu shi ne a samu ingantatticiyar gwamnati a kasar nan,” in ji shi.
Ya jaddada cewa sarakuna ba su da karfin da zasu tilasta wani, musamman gwamnati ta zartar da wata doka a kasar nan, amma suna iya bada shawara domin shugabanci ba na mutum guda ba ne na kowa da kowa ne.