Gazawar shugabanni ke haddasa rashin tsaro a kasa – Sultan

Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa gazawar shugabanni ce ta kawo rashin tsaro a kasar nan, domin kuwa a cewarsa idan shugabanni suka mike tsaye ta hanyar zartar da abin da ya da ce, za su magance matsalar. Ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wajen taron majalisar Sarakunan Arewacin kasar nan […]

Gazawar shugabanni ke haddasa rashin tsaro a kasa – Sultan

Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa gazawar shugabanni ce ta kawo rashin tsaro a kasar nan, domin kuwa a cewarsa idan shugabanni suka mike tsaye ta hanyar zartar da abin da ya da ce, za su magance matsalar.

Ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wajen taron majalisar Sarakunan Arewacin kasar nan da aka gudanar a Kaduna a Litinin din da ta gabata.

Ya ce a matsayinsa na shugaban Fulanin kasar nan da kuma yankin Afirka ta yamma, ba zai taba yarda ya umurci wani Bafulatani ya dau makami ya kashe wani mutum ba.

Kan haka sai Sultan din ya ce masu kashe mutane da sunan Fulani, ’yan ta’adda ne kuma ana iya samunsu a kowace kabila.

“Idan ka ga abubuwa irin wannan na faruwa, akwai gazawar shugabanni wajen aiwatar da ayyukansu, domin idansuna yin abin da ya dace, hakan ba zai faru ba.

“Mun dade muna kira ga jama’a da su zauna lafiya, su bar hukuma ta dauki mataki, mu kuma za mu ci gaba da matsa wa hukuma har sai sun dau matakan da za su kawo maslaha ga irin wadannan matsaloli. 

“A matsayina na shugaban Fulani, ba zan taba yin kira ga Fulani su dauki makami su kai wa wani hari ba da nufin kashe shi. Na zauna da mutane masu yawa na kuma san matsalolinsu. Don haka ba zan taba yarda Bafulatani ya dau makami ya kashe wani ba.

“Na jima ina cewa a wuraren taruka irin wannan cewa duk masu daukar makami suna kashe mutane ’yan ta’adda ne koma waye. Ko Inyamuri ne ko Bayarbe ko kuma Bahaushe ko Fulani, ba ka da ’yancin kashe wani mutum,” inji shi.

Sultan ya kuma bayyana cewa halartar sarakunan Kudancin kasar nan wajen taron, alama ce da ke nuna kasancewarsu ’yan kasa daya al’umma daya. 

“Yan uwanmu daga Kudu sun halarci taron nan ne domin mun yarda mu zauna tare a matsayin ’yan kasa daya kuma al’umma daya. Burinmu shi ne a samu ingantacciyar gwamnati a kasar nan,” inji shi.

Ya jaddada cewa sarakuna ba su da karfin da za su tilasta wani musamman gwamnati ta zartar da wata doka a kasar nan amma suna iya ba da shawara domin shugabanci ba na mutum daya ba ne, na kowa da kowa ne.