Gbagyi sun shigar da kara kan nada sabon Sarkin Bwari
Wasu jagororin kabilar Gbagyi a yankin Bwari na birnin tarayya Abuja sun shigar da kara a babban kotun birnin tarayya inda suke neman kotun da ta soke nadin da ministan birnin malam Muhammad Musa Bello ya yi na tabbatar da Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro a matsayin sabon sarkin Bwari. Da ya ke tabbataar da lamarin […]
Wasu jagororin kabilar Gbagyi a yankin Bwari na birnin tarayya Abuja sun shigar da kara a babban kotun birnin tarayya inda suke neman kotun da ta soke nadin da ministan birnin malam Muhammad Musa Bello ya yi na tabbatar da Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro a matsayin sabon sarkin Bwari.
Da ya ke tabbataar da lamarin ga Aminiya a ranar Litinin da ta gabata, Esu Bwari J.P Ibrahim Yaro ya ce karar wadda aka shigar a ranar Alhamis ta makon jiya ya biyo bayan korafi ne da jama’arsa su ka yi a kan nadin wanda minstan ya tabbatar a ranar Talata ta makon jiya.
Esu Bwari ya ce “Ni a kashin kaina ban da wata niyar daukan mataki a kan lamarin, na bar wa Allah komi kamar yadda na shaida maka a baya, amma kasancewar jama’ar da ke karkashina su ke da ni, ba ni ke da kaina ba, su ne su ka doge a kan neman hakkinsu kuma a dalilin hakan ban da wani zabi na hana su.
A bangaren fadar sarkin Bwari bukukuwa da ziyarar taya murnar nadin na kara kankama inda izuwa ranar Litininin da ta gabata sarakuna da sauran shugabannn al’umma da dama sun ziyarci fadar.
Hakimin Dutsen-Alhaji wanda ke karkashn kasar Bwari Alhaj Abubakar Bako shi ne ya fara kai ziyarar a tsakanin daukacin sarakunan Abuja, inda ya je fadar tun a ranar da aka sanar da nadin. Sai mai martaba sarkin Keffi daga Jihar Nassarawa Dokta Shehu Muhammad Cindo Yamusa wanda ya kai tasa ziyarar kwana guda bayan sanarwar. kanin sabon sarkin kuma wanda yanzu aka bai wa mukamin chiroman Bwari mukamin da sarki ya rike gabanin ya zama sarki, mai suna Alhaji Abubakar Musa Ijakoro.
Sauran sarakunan da suka ziyarci fadar sun hada da Agoran Zuba Alhaji Muhammad Bello Umar, sai sarkin Jama’a daga Jihar Kaduna da kuma na Zimigili daga Jihar Nassarawa. Shugaban karamar hukumar Bwari mista Musa Dikko da takwaransa na karamar hukumar birnin Abuja da kewaye AMAC Malam Abdullahi Adamu Kandido suma sun kai ziyarar, a yayin da uwargidan shugaban kasa hajiya A’isha Buhari ta aika da tawagar taya murna a karkashin jagorancin babbar mai taimakamata hajiya Hajo Sani.