Gbajabiamila ya yi ta’aziyyar mutuwar tsohuwar shugabar matan APC, Kemi Nelson
Tsohuwar shugabar matan ta jam’iyyar APC ta rasu a ranar Lahadi.
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Misis Kemi Nelson, wacce ta taba zama shugabar mata ta jam’iyyar APC a yankin Kudu maso Yamma.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya bayyana marigayiya Misis Nelson a matsayin daya daga cikin ginshikan jam’iyyar APC a Jihar Legas da Najeriya baki daya, inda ya ayyana mutuwarta a matsayin babban rashi.
- NAJERIYA A YAU: PDP Ta Yi Waje Da APC A Osun
- Chelsea ta sayi dan wasan bayan Napoli Kalidou Koulibaly
Ta kasance tsohuwar kwamishina a Jihar Legas kuma har zuwa rasuwarta, mamba ce a majalisar masu bada shawara ga gwamnan Jihar Legas (GAC).
Nelson, wadda tsohuwar Babbar Darakta ce ta Hukumar Inshora ta Najeriya (NSITF), ta rasu ranar Lahadi tana da shekaru 66 a duniya.