Geidam ya nad-a masu ba shi shawara

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam ya hori sababbin masu ba shi shawara na musamman da ya nada da su zama masu ba shi shawarwari nagari kuma masu amfani a duk bangarorin da aka tura su.Gwamna Gaidam ya bayyana haka ne  a cikin jawabinsa lokacin da yake  rantsar da sababbin masu ba shi shawarar su […]

Geidam ya nad-a masu ba shi shawara
Geidam ya nad-a masu ba shi shawara

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam ya hori sababbin masu ba shi shawara na musamman da ya nada da su zama masu ba shi shawarwari nagari kuma masu amfani a duk bangarorin da aka tura su.
Gwamna Gaidam ya bayyana haka ne  a cikin jawabinsa lokacin da yake  rantsar da sababbin masu ba shi shawarar su 10 da aka yi a Gidan Gwamnatin Jihar da ke garin Damaturu.
Gwamnan ya kara da cewa, su dauki matsayin da aka ba su a bisa ga cancanta tare da amincewar masu ruwa da tsaki kan harkokin jihar inda aka yi la’akari da tarihinsu da gaskiyarsu don haka su zage dantse don ganin sun ba marada kunya ta wajen ba da shawarwarin da za su ciyar da jihar gaba.
“Baya ga ba da shawarwarin ciyar da jihar gaba har wayau akwai bukatar a matsayinku na ’yan siyasa ku zama masu kusantar al’ummominku don jin koke-kokensu domin ba da shawara kan yadda za a magance su,” inji Gwamnan.
Wasu daga cikin masu ba da shawarar dai sun hada da Kyaftin Bilal Bulama (mai ritaya), Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro, sai Barista Aliyu Shehu Abubakar, Harkokin Shari’a da Alhaji Lawan Shettima Ali kan Harkokin ’Yan majalisa da siyasa da kuma Alhaji Mai Aliyu Usman kan Harkokin Ilimi.
Gwamnan ya kuma nada Alhaji Hamidu Ali a matsayin Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar da kuma mambobi biyu a Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Jihar (SIEC), wadanda nan take aka rantsar da su.