George Weah ya zama dan kwallo na farko da ya zama Shugaban kasa a duniya
A ranar Litinin da ta gabata ne aka rantsar da George Weah a matsayin sabon Shugaban kasar Laberiya. Akalla shugabannin kasashe takwas ne daga yankin Afirka suka halarci bikin rantsarwar, ciki har da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo. Haka nan kuma zaratan ‘yan kwallon kafa sun yi tururuwa […]

A ranar Litinin da ta gabata ne aka rantsar da George Weah a matsayin sabon Shugaban kasar Laberiya.
Akalla shugabannin kasashe takwas ne daga yankin Afirka suka halarci bikin rantsarwar, ciki har da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Haka nan kuma zaratan ‘yan kwallon kafa sun yi tururuwa zuwa filin rantsarwar domin taya daya daga cikinsu murnar zama dan kwallo na farko da ya zama Shugaban kasa a tarihin duniya.
Shi dai George Weah ba yau ya fara kafa tarihi a yankin Afirka ba, domin a bangaren taka leda ma, shi kadai ne dan Afirka da ya taba zama gwarzon dan kwallon duniya.
Weah ya yi fice sosai a cikin ‘yan kwallo a tsakanin shekarun 1999, sannan kuma ya yi akalla shekara 13 yana fafutuka a siyasar kasar Laberiya har ya zama Shugaban kasa bayan ya kasance sanata a Majalisar Dattawan kasar.
dan shekara 51 a rayuwa, George Weah ya buga wa kungiyoyin AC Milan, inda ya fi yin fice har ya samu damar lashe gwarzon dan kwallon duniya a shekarar 1995.
Ya fara zama fitaccen dan wasa ne yana dan shekara 21 lokacin da kocin Arsenal, Arsene Wenger ya gano shi a lokacin yana buga wa wata kungiya a kasar Kamaru.
Wenger ne ya yi sanadiyar zuwansa nahiyar Turai, inda daga bisani ya buga wa kungiyoyin AS Monaco, PSG, AC Milan, Chelsea, Manchester City da Olympikue Marseille. Wannan ne ya sa Geoge Weah yake cewa Arsene Wenger kamar uba yake a gare shi.
Duk da ficen da ya yi a fannin taka leda, George Weah bai manta da kasarsa ba wadda ta yi fama da yakin basa-basa na tsawon lokaci wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum kusan 250,000 kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ya kasance yana biyan ‘yan wasan kasar Laberiya da kudinsa domin su samu damar fita wasa a kasashen waje. Wannan ya sa wasu daga cikin abokanan wasansa suke masa kallon mutumin kirki, har ma wani mai suna Thomas Kojo yake cewa, “Yanayin yadda George Weah ke son kasar Laberiya abin mamaki ne,” kamar yadda ya shaida wa Reuters.
Daga bisani sai George Weah ya fada harkar taimakon al’umma baki daya ba sai ‘yan kwallo ba kawai. Hakan ya sa har ya zama ambasadan Asusun Kula Da kananan Yara na Majalisar dinkin Duniya wato Unicef a kasar.
Ya sha fama da gwargwarmaya da tsohon Shugaban kasar, Charles Taylor wanda yake kallon cewa Weah na hangen kujerarsa ne kafin ya bar kujerar shugaban kasar a shekarar 2013.
George Weah ya shiga hakar siyasa tsundum bayan ya yi ritaya daga kwallo kafa. Domin ya cimma bruinsa, sai ya kafa Jam’iyyarsa ta Congress for Democratic Change a shekarar 2005, sannan ya yi takarar neman shugabancin kasa a shekarar, inda tsohuwar Shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ta kayar da shi a zagaye na biyu.
Wannan rashin nasarar bai dakatar da George Weah daga tsayawa takarar ba, domin a shekarar 2011 ma sai da ya sake tsayawa takara a matsayin mataimakin Shugaban kasa tare da mai neman shugabacin a wannan lokacin mai suna Winston Tubam, nan ma suka sake yin rashin sa’a. sai a shekarar 2014 ya samu nasarar zama sanata a Majalisar Dattawar kasar mai wakiltar yankin Monterrado.
Sannan kuma ya sake yin takarar neman shugabancin kasar bara, inda ya samu nasarar kayar da mataimakin Shugaban kasar wanda ya bar gado Joseph Boakai, sannan aka rantsar da shi a ranar 22 ga watan Janairu.
George Weah yana da mata Clar Weah, sannan kuma dansu mai suna Timothy ya gaje mahaifinsa ne a fagen taka leda domin yanzu haka yana buga wa kungiyar PSG da ke kasar Faransa.