George Weah ya zama Sanata a Laberiya

Tsohon Gwarzon dan kwallon duniya kuma haifaffen Laberiya George Weah ya zama Sanata a zaben da aka yi a Laberiya a karshen makon jiya.  Ya samu nasarar lashe zaben ne bayan ya doke abokin takararsa kuma dan Shugaban kasar Laberiya Robert Sirleaf.Da wannan nasarar da tsohon dan kwallon ya samu, zai samu karfin gwiwa a […]

George Weah ya zama Sanata a Laberiya
George Weah ya zama Sanata a Laberiya

Tsohon Gwarzon dan kwallon duniya kuma haifaffen Laberiya George Weah ya zama Sanata a zaben da aka yi a Laberiya a karshen makon jiya.  Ya samu nasarar lashe zaben ne bayan ya doke abokin takararsa kuma dan Shugaban kasar Laberiya Robert Sirleaf.
Da wannan nasarar da tsohon dan kwallon ya samu, zai samu karfin gwiwa a zaben Shugaban kasar da za a yi a shekarar 2017 a inda ake sa ran zai  sake yin takarar shugabancin kasar.
George Weah ya samu nasarar ce bayan ya lashe kashi 78 daga cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada.
George Weah, jigo ne a jam’iyyar adawa ta Congress for Democratic Change (CDC), shugaban kasa Ellen Johnson Sirleaf ta doke shi ne  a zaben shugaban kasa  a shekarar 2005 sannan ya sake shan kaye daga wajenta a zaben shugaban kasa karo na biyu a shekarar 2011.   Yanzu kuma ana sa ran zai sake yin takara a zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar 2017.
George Weah dai ya zama Gwarzon dan kwallon Duniya ne a shekarar 1995 kuma shi ne dan Afirka tilo da aka taba zaba a wannan matsayi a tarihin gasar.
kasar Laberiya dai tana fama da matsalar cutar Ebola inda kawo yanzu an samu mutuwar akalla mutum 3,300.  Kafin bullar cutar Ebola kasar ta yi fama da tashe-tashen hankulan siyasa da na kabilanci.
Tuni George Weah ya bayyana farin cikinsa a kan wannan zabe da aka yi masa, kuma ya sha alwashin ba marada kunya a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai jim kadan bayan an bayyana sakamakon zaben.