Gerbinho zai koma kulob din Aljazira
Rahotanni da ke fitowa daga Italiya sun nuna dan kwallon AS Roma kuma haifaffen Kwaddebuwa Gerbinho ya kusa canza sheka zuwa kulob din Al-Jazira da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Rahoton ya ce tuni kulob din ya taya Gerbinho a kan Yuro miliyan 13 kwatankwacin Naira biliyan 3 da miliyan 237. A kwanakin baya ne dai […]
Rahotanni da ke fitowa daga Italiya sun nuna dan kwallon AS Roma kuma haifaffen Kwaddebuwa Gerbinho ya kusa canza sheka zuwa kulob din Al-Jazira da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Rahoton ya ce tuni kulob din ya taya Gerbinho a kan Yuro miliyan 13 kwatankwacin Naira biliyan 3 da miliyan 237.
A kwanakin baya ne dai Daraktan kula da wasanni na kulob din Roma Walter Sabatini ya gana da Shugaban kulob din Al-Jazira Ammar Al Bashir a Italiya inda suka tattauna batun cinikin dan kwallon.
Gerbinho dan kiumanin shekara 28 ya taba buga wa kulob din Beberen da na Le Mens da Lille dukkaninsu da ke Faransa kafin daga bisani ya koma kulob din Arsenal na Ingila. Daga nan ne kuma ya koma na kulob din AS Roma da ke Italiya.
Yana daga cikin ’yan kwallon Kwaddebuwa da suka lashe gasar cin kofin Afirka na bana. Ya zura wa kulob din AS Roma kwallaye biyu ne kacal daga wasanni 24 da ya yi a kakar wasa ta bana. Amma a shekarar 2011 ya zura kwallaye 15 daga cikin wasanni 35 da ya yi wa kulob din.
Rahoton ya kara da cewa akwai yiwuwar kulob din Al-Jazira ya ninka wa Gerbinho albashin da yake karba a AS Roma na Yuro miliyan biyu da dubu 900 a shekara idan ya amince ya koma kulob din.