Gerrard ya yaba kwazon Aribo dan wasan da Super Eagles ta gayyata
Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Rangers ta kasar Scotland, Steben Gerrard ya yaba kwazon Joe Aribo a wasansu da kungiyar East Fife wanda Rangers din ta lallasa da ci 3-0 a ci gaba da gasar rukuni-rukuni ta kasar Scotland. Dan wasan na tsakiya ya nuna matukar kwazon da ya taimaka wajen hayewa da kungiyarsa zuwa […]
Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Rangers ta kasar Scotland, Steben Gerrard ya yaba kwazon Joe Aribo a wasansu da kungiyar East Fife wanda Rangers din ta lallasa da ci 3-0 a ci gaba da gasar rukuni-rukuni ta kasar Scotland.
Dan wasan na tsakiya ya nuna matukar kwazon da ya taimaka wajen hayewa da kungiyarsa zuwa gasar rukuni na kasar. Wannan ne ya sanya tsohon dan wasan Liberpool kuma tsohon Kyaftin din Ingila, Gerrad ya yaba wa dan wasan mai shekara 23.
“Kowa yana maganar kwazon da Joe Aribo ya nuna, kuma hakan ya yi daidai.” Gerrard ya fada wa Gidan Talabijin na BT Sport. Ban san iyakar ’yan wasa managarta da suka taba nuna bajinta a wannan filin wasan ba, amma dai ina tabbatar muku samun irin Joe ba karamin aiki ba ne.
Kwararrun ’yan wasa ba sa boyuwa koda suna wasa ne a gaban mutum dubu 50, ko a mutum 1,500 a wurinsu duk abu guda ne. Joe ya nuna irin wannan kwarewa tun a ranar farko da ya fara wasa a nan. Bai boye kansa ba tun daga farkon wasa har karshensa,” inji Gerrad.
Aribo ya koma Rangers ne bayan da ya bar Kungiyar Charlton Athletic ta Ingila a karshen kakar bana, inda a yanzu ya sanya hannu kan kwantaragin shekara hudu da Rangers, wannan na nufin zai zauna a filin wasa na Ibrod har karshen shekarar 2023.
Aribo wanda tuni aka gayyace shi zuwa Kungiyar Super Eagles, ana sa ran zai fara buga wa Najeriya wasa a wasan sada zumunta da Najeriya za ta yi da kasar Ukraine a ranar 10 ga watan Satumban bana.