Ghali Na’Abba: Muhimman Abubuwa 10 da ya kamata ku sani

Shugaban Majalisar Wakilai da ya yi taka wa Obasanjo burki, har shugaban kasan ya nemi tsige shi, amma ya kasa, har sai da ya kammala wa’adinnsa na shugabancin majlaisar

Ghali Na’Abba: Muhimman Abubuwa 10 da ya kamata ku sani

Ghali Umar Na’Abba

A ranar Laraba 27 ga Disamba, 2023 Allah Ya yi tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Alhaji Ghali Umar Na’abba rasuwa.

Shin kun san cewa Ghali Na’Abba shi ne Shugaban Majalisar Wakilai da ya yi taka wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo burki, har shugaban kasan ya nemi a tsige shi, amma ya kasa?

Ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da marigayin:

1. An haifi Ghali Na’Abba ne a unguwar Tudun Wada da ke Kano a ranar 27 ga watan Satumba, 1958, kuma mahaifinsa dan kasuwa ne kuma malamin addinin Musulunci.

2. A 1969 Ghali Na’Abba ya kammala karatun firamare a makarantar firamaren Jakara, sannan ya kammala Sakandare a Kwalejin Rumfa a 1974, da kuma Makaranar sharar fage a 1976, duk a Kano.

3. Ya karanci Ilimin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Ahmdau Bello (ABU) da ke Zariya a 1979, inda a lokacin da yake dalibi, ya kasance wakilin dalibai ’yan Jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano a jami’ar.

4. Bayan dawowar Najeriya kan tsarin dimokuradiyya a Jamhuriya ta Hudu a 1999, Ghali Na’Abba ya zama dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Karamar Hukumar Birnin Kano a Majalisar Wakilai daga 1999-2003.

5. Da farko ya nemi tsayawa takarar shugaban majalisar kuma ya samu goyon bayan takwarorinsa, sai dai daga bisani ya fuskanci masin lamba, ya janye wa Honorabul Ibrahim Salisu Buhari daga Jihar Kano, wanda ya yi nasara a matsayin shugaban majalisar na bakwai kuma na farko a Jamhuriya ta hudu.

6. Ghali Umar Na’Abba ya kasance Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai a zamanin shugabancin Ibrahim Salisu Buhari.

7. Bayan ’yan watanni Ghali Umar Na’Abba ya Shugaban Majalisar Wakilai na takwas, bayan Ibrahim Salisu Buhari ya yi murabus daga kujerar kan badakalar takardar shaidar karatun bogi.

8. Zamansa shugaban majalisar ke da wuya ya sanar ayyana shirinsa na cin gashin kan bangaren majalisar.

9. Ya samu goyon bayan sama da 300 daga cikin mambobin majalisar su 360 wajen taka wa Obasanjo buki kan kudurin dokar hukumar NDDC da sauransu.

10. Sakamakon haka, dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Obasanjo, har shugaban kasan ya nemi a tsige shi, amma duk da haka sai da Ghali ya kammala wa’adinsa na shekaru hudu.

Shekaru 20 bayan saukarsa daga kujerar Shugaban Majalisar Wakilai Allah Ya yi masa rasuwa a dalilin jinya, kuma har yanzu ana buga misali da shi wajen saita shugabannin siyasa da kuma taka musu burki daga yin kama-karya.

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja