Ghana da Najeriya: Allah daya gari bamban
Shin da me za a fassara matakin da Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya dauka a Juma’ar makon jiya, inda ya kori wata ministarsa daga aiki, kawai don an zargi cewa ta sanya wa kanta wani kuduri? An kore ta ne kuma ba tare da an gudanar da bincike, an tabbatar da laifin nata […]
Shin da me za a fassara matakin da Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya dauka a Juma’ar makon jiya, inda ya kori wata ministarsa daga aiki, kawai don an zargi cewa ta sanya wa kanta wani kuduri? An kore ta ne kuma ba tare da an gudanar da bincike, an tabbatar da laifin nata ba. Lallai kam wannan aiki na Shugaban kasa, akwai wata caca bayan tiya, domin kuwa muna sane da cewa cikin sharuddan da kungiyar kasashen ECOWAS ta gindaya, har da cewa ba za a doka wa mutum hukunci ba kafin bincike.
Matakin da aka dauka a Ghana, zai dade yana ba mutane mamaki, musamman ma ’yan siyasa a Najeriya. daya daga cikin irin wadannan misalai, shi ne raguwar shaidar da aka samu, wadda ta sa har aka kori Mataimakiyar Ministar Sadarwa ta Ghana, Mis bictoria Hammah. Wannan raguwar shaida kuwa ita ce, wai an samu wani bayani ne, wanda aka nada cikin sirri kuma aka yada shi a intanet. Mu tuna, ko a kwanakin baya, an samu irin wannan bayani a Najeriya, wanda aka yi ta yadawa a intanet amma nan batun ya tsaya, babu abin da ya faru. Kai hasali ma, a Najeriya, irin wadannan bayanai, koda sun kai kala dubu, in dai a intanet ne aka yada su, babu abin da za su haifar a Najeriya, balle ma har a ce guda daya ya haddasa an kori minista kacokan. A Najeriya, inda za ka ga an baza hotunan motocin da ake ikirarin an yi aringizo da almundahana wajen sayen su, an buga takardun shaidar sayen motocin, an buga bayanai masu karo da juna tsakanin jami’an da ke wa batun kariya da sauran duk irin wadannan batutuwa da ke nuna tabargaza amma duk da haka babu abin da haka za ta haifar, kuma ba za su sanya a kori minista daga aikinta ba, a Najeriya.
Su a ganin ’yan siyasar Najeriya, irin yadda Shugaban kasar Ghana ya kori ministarsa cikin hanzari, babban abin kunya ne. An kori wannan ministar daga aiki ne cikin kasa da awa 24 da samun fitar labarin abin kunyar da ta fada. An baza maganar ce a intanet kuma Shugaba Mahama bai yi wata-wata ba ya dauki mataki. Bai jira ’yan majalisar kasarsa sun fara wani bincike ba. Idan da a Najeriya ne, koda majalisar ma ta gayyaci irin wannan minista domin bincike, shugaban na iya tura ta kasashen waje, a tura wani jami’in daga ma’aikatarta ya wakilce ta a zaman majaisar. Kuma da Shuagabn kasar Ghana ya so, zai iya koyi da takwararnsa na Najeriya, ya yi biri-biri, ya ce shi ma ya kafa nasa binciken ministar, wanda haka zai dauke hankalin majalisa daga yin nata binciken. Daga bisani kuma batun ya shiririce.
Abin da ma ya kamata mu tambaya shi ne, shin mene ne takamaimai laifin da Mis Hammah ta aikata? Amsar tambayar nan, ita ce za ta girgiza jami’an gwamnati a Najeriya saboda mamaki. Ministar, ba a samu rahoto ko labarin cewa ta saci kwabon kowa ba kuma ba ta ma yi wani yunkuri mai kama da haka ba. Abin da kawai ta yi shi ne, ta bayyana niyyarta ce, cewa za ta aikata haka. A nan Najeriya, abin da kawai za a ce ta yi shi ne, niyyar yin ha’inci, wanda kuma ba ta kai ga yi ba. Abin da kawai Minista Hammah ta yi shi ne, an saci daukar hirar da ta yi ce a kaset, inda aka ji tana ba kawarta Mataimakiyar Minista, Rachel Appoh labari. A hirar, ta fadi cewa: “Na fada wa Rachel cewa ni na fahimci siyasa sosai… ba zan taba barin siyasa ba har sai na mallaki dala miliyan daya. Idan ka samu kudi masu yawa, daga nan za ka mallaki mutane.” Shi ke nan laifin da ta aikata.
Abin da dan siyasar Najeriya zai yi idan ya ji wannan labarin shi ne, zai yi matukar mamaki, sannan ya fahimta da cewa lallai ’yan siyasar Ghana ba su da babban buri in dai ta bangaren tara dukiya ne. Idan ba haka ba, ta yaushe za a ce Minista sukutum amma tana da burin mallakar dala miliyan daya kacal bayan ta kwashe shekaru a kujera? A Najeriya, Shugaban karamar Hukuma ne zai yi wannan burin. Ko shi ma, idan wani ya ji zai ce shi tsohon yayi ne ko kuma ma a kira shi da sunan bakauye, kidahumi; domin burin nasa ya kasa na takwarorinsa ’yan zamani.
A Najeriya, idan babban dan siyasa, wanda ya dade a kan mulki ya sauka alhali ya mallaki dala miliyan daya kacal, sannan ya ce zai zauna a Abuja, domin gudanar da matsakaiciyar rayuwa, to kuwa nan da ’yan watanni zai tsiyace karkaf. Domin kuwa kafin ya ankara, a sakamakon tsadar rayuwa, ba zai san inda wannan dala miliyan daya ta makale ba.
Za mu ci gaba